‘Akwai Matsaloli Biyu’: Tsohon Gwamnan CBN Ya Ce Babban Bankin Kasa Ya Yi Kuskure Wajen Sauya Kudi

‘Akwai Matsaloli Biyu’: Tsohon Gwamnan CBN Ya Ce Babban Bankin Kasa Ya Yi Kuskure Wajen Sauya Kudi

  • Kingsley Moghalu, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin gwamnan CBN ya ce akwai kura-kurai biyu game da sauyin fasalin Naira
  • Ya bayyana cewa, kitimurmurar da ta biyo bayan sauyin kudin nan ba komai bane face gazawa wajen tsara yadda sauyin zai zama
  • A fahimtar Moghalu, sabuwar dokar kudi tana da kyau, amma akwai lam’a da kura-kurai da ke tattare da yinta, duba da yin hakan kusa da zabe

Daya daga cikin tsoffin mataimaka gwamnan CBN, Kingley Moghalu ya bayyana rashin jin dadinsa game da kunci da rikicin da ya biyo bayan batun sauyin kudi na babban bankin kasar.

Moghalu ya bayyana cewa, duk wani kunci da ‘yan Najeriya ke ciki ba komai bane face kuskuren da CBN ya yi wajen tsara yin sabuwar dokar kudi.

Hakazalika, ya ce tsoma baki da kotun kasar ya yi game da batun sauyin ya nuna matsala da kuma shigar siyasa cikin lamuran da bai kamata a kawo siyasa ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya, zai shafi Najeriya

Yadda sauyin kudi ya zo da matsala a fahimtar tsohon gwamnan CBN
Yadda lamarin kudi ke ci gaba da daukar hankali a Najeriya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Moghalu ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, sauyin kudi da kula da takardun kudi nauyi ne da ya rataya a wuyan babban bankin, kuma shi dai bai da matsala da hakan sai ta hanyoyi biyu kacal.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kura-kurai biyu da ke tattare da batun sauyin kudi a fahimtar Moghalu

Ya bayyana cewa, matsala ta faro dai ita ce wa’adin kwanaki 90 da CBN ya bayar na daina amfani da tsoffin kudi bai yi ba, hakazakila, na biyu kuma yin sauyin kusa da zabe.

Ya shaida cewa, da ya kamata a bi da sauyin ne a hankali sabanin yadda aka yi shi cikin gaggawa ba tare da la’akari da wasu lamurra ba.

A cewarsa:

“Sai kuma a gaba, ya zama batun ‘sahihi kuma zabe na gaskiya’ don dakile siyan kuri’u”

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

'Yan siyasa sun ji kamar dasu ake

A fahimtarsa, dalilin da CBN ya bayar na cewa za a magance siyan kuri’u shi ne ya sake dama lamarin kasar.

Moghalu ya ce, ‘yan siyasa sun yi tsalle sun yi kokarin a tsawaita wa’adin ne saboda suna ganin an nufi dakile wani abu da suke shiryawa ne.

A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnan jihar Ogun yace zai rufe duk wani bankin da ya daina karbar tsoffin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.