Yahudawan Najeriya Sun Kai Kara Kotu Kan Sanya Zabe Ranar Asabar Saboda Ranar Ibadarsu Ce
- Cocin addinin Yahudawa a Najeriya ya shigar da kara a gaban kotu game da zabukan da ake yi a Najeriya a ranakun Asabar
- Cocin ya koka kan yadda ake yin zabukan Najeriya a ranakun Asabar da kuma jarrabawar daban-daban
- Kotun ya bayyana matsayarsa, kana ya amince da a duba lamarin Yahudawan kasar don mutunta addininsu
FCT, Abuja - Mai shari’a James Omotosho na babban kotun tarayya da ke Abuja ya sanya ranar 22 ga watan Maris don sauraran karar da cocin Yahudawa na Seventh-day Adventish ya shigar.
Ugochukwu Uchenwa, wani mamban cocin ya shigar da karar ne don neman kotun ya hana gudanar ayyukan zabe da dukkan nau'ikan jarrabawa a Najeriya a ranakun Asabar.
A zamansa na jiya Laraba, kotun ya ba shugaba Buhari da atoni-janar na kasa, wadanda su ake kara lokaci don duba lamarin da aka bijiro dashi, Leadership ta ruwaito.
Hakazalika, kotun ya amince da bukatar lauyan mai shigar da kara, Benjamin Amaefule kan batun da mamban cocin ya shigar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abin da yasa mamban Yahudawa ya shigar da kara
Uchenwa ya bayyana cewa, yin zabuka a Najeriya a ranakun Asabar daidai yake da take masu ‘yancinsu na addini a matsayinsu na Yahudawa ‘yan Najeriya.
Hakazalika yin jarrabawa kamar WAEC, NECO da JAMB da dai sauransu duk a ranakun na shiga 'yancinsu na addini.
Ya bukaci kotun da Ya rushe yadda ake sanya ranakun zabe su kasance Asabar a Najeriya saboda rana ce ta bauta ga cocin na Seventh-Day Adventish.
Haka nan ga jarrabawa, ya nemi a daina sanya ranakun Asabar, kamar yadda rahoton jaridar Daily Post ya tattaro.
A madadin haka, mamban cocin ya bukaci a tursasa gwamnati da ta ba Yahudawan Najeriya damar yin zabukan a ranakun da ba na Asabar a cikin mako.
Jerin wadanda Yahudawan ke kara
Rahoton da muka samo daga jaridar Leadership ya bayyana adadin wadanda ake kara kamar haka:
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Atoni-janar/ministan shari’a na Najeriya
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)
- Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB
- Hukumar shirya jarraba ta kasa (NECO)
- Hukumar shirya jarrabawa ta Yammacin Afrika (WAEC)
- Hukumar jarrabawa ta NABTEB
Yahudanci na daya daga cikin addinai mafi dadewa a Najeriya, amma duk da haka akwai karancinsu a Najeriya.
A bangare guda, addini mafi kara yaduwa a duniya addinin Islama ne, wanda har a kasashen Turai ya kara yawan mabiya.
Asali: Legit.ng