IPOB Ta Shiga Jerin Kungiyoyin Yan Ta'adda 10 Mafi Hatsari a Duniya
Rahoton ta'addanci na duniya (GTI) ya sanya IPOB a cikin jerin ƙungiyoyin yan ta'addda 20 masu haɗari a duniya.
Ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB) ta kai matsayi na 10 a cikin jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda mafi haɗari a faɗin duniya.
Makarantar tattalin arziki da kuma bin diddigin ayyukan ta'addanci a duniya ce take wallafa rahoton GTI. A sabon rahoton da ta fitar ranar Talata 14 ga watan Maris, IPOB na matsayi na 10.
Jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda 20 mafi hatsari a duniya
Matsayi | Sunan kungiya | Adadin kisa | Hare-hare | Yawan masu rauni |
1 | IS | 1045 | 410 | 644 |
2 | Al-shabaab | 784 | 315 | 1016 |
3 | IS ta lardin Khorasan | 498 | 141 | 132 |
4 | Jama'atu Nusrat Islam (JNIM) | 279 | 77 | 215 |
5 | Balochistan Liberation Army (BLA) | 233 | 30 | 113 |
6 | Islamic State West Africa (ISWAP) | 219 | 65 | 118 |
7 | Boko Haram | 204 | 64 | 51 |
8 | Taliban ta Pakistan | 137 | 90 | 187 |
10 | Yan awaren IPOB | 57 | 40 | 16 |
11 | Kurdistan Workers Party (PƘK) | 40 | 54 | 150 |
12 | Communist Party a Indiya | 39 | 61 | 30 |
13 | Al-Qaeda ta yankin larabawa (AQAP) | 17 | 6 | 23 |
14 | FARC ta ƙasar Colombia | 16 | 17 | 37 |
15 | New Peoples Army (NPA) | 19 | 13 | 25 |
16 | Ƙungiyar LeT | 8 | 6 | 38 |
17 | Balochistan Liberation Front (BLF) | 6 | 4 | 8 |
18 | National Liberation Army (ELN) | 5 | 28 | 77 |
19 | Islamic Jihad | 5 | 2 | 10 |
20 | Belochistan Republic Army | 4 | 1 | 8 |
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
IPOB ta kafa tarihin a shekarar 2022 - GTI
A cewar rahoton aikata ta'addanci na duniya (GTI), ƙungiyar IPOB ta kaddamar da hare-hare da kashe-kashe mafi yawa a tarihinta a shekarar 2022.
"Kungiyar IPOB, wacce gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci ta aikata ta'asa mafi muni a 2022. Su ke da alhakin kai hare-hare 40 da kisan 57 a 2022."
"Hakan ya nuna an samu karin hare-hare 26 da kisan mutane 34 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci 2022," inji rahoton.
A wani labarin kuma Najeriya ta koma matsayi na 36 a jerin kasashe masu karfin sojoji 145 na faɗin duniya
A sabon rahoton da aka fitar, Najeriya ta samu koma baya da matsayi ɗaya, daga matsayi na 35 zuwa matsayi na 36 a duniya.
Haka zalika a jerin kasahen nahiyar Afirka, Najeriya ta sake matsawa baya da matsayi ɗaya a sabon rahoton.
Asali: Legit.ng