Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya
- Gwamnatin Najeriya ta dage fara aikin kidiya yan kasa na shekarar 2023 da aka yi shirin farawa a watan Maris zuwa Mayu
- Alhaji Lai Mohammmed, Ministan Labarai da Al'adu na kasa ne ya bayyana hakan a yau Laraba 15 ga watan Maris bayan taron FEC
- Mohammed ya ce an dage kidayar jama’a ne saboda sauya jadawalin zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha zuwa ranar 18 ga Maris
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta matsar da fara yin aikin kidaya yan kasa na shekarar 2023 zuwa watan Mayun 2023.
Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, a ranar Laraba, ya bayyana hakan a Abuja bayan taron majalisar zartarwa wato FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da farashin kayayyaki ya kara hawa a Najeriya daidai karancin Naira
A cewarsa, za a yi kidayar a watan Mayu.
A baya, The Punch ta rahoto cewa za a fara kidayar a ranar 29 ga watan Maris.
Abin da ya sa aka dage yin kidayar ta shekarar 2023 - Lai Mohammed
Ministan ya ce ya zama dole a dage fara aikin kidayar ne saboda sauya ranar yin zabukan gwamnonin jihohi zuwa ranar 18 ga watan Maris.
Mohammed ya ce majalisar zartaswar ta amince a ware naira biliyan 2.8 ga Hukumar Kidayar ta Kasa, NPC, domin ta siyo wasu manhajoji da za a yi amfani da su wurin aikin.
Ya ce:
"Akwai takardar da Hukumar Kidaya ta Kasa ta gabatar na neman siyan wasu manhajoji da za su yi amfani da su wurin kidayar a watan Mayun wannan shekarar. Na yi imanin cewa saboda sauya ranar zabe, ba za su iya fara kidayar kamar yadda aka shirya ba a farko.
"Sun nemi izinin majalisar a bada kwangilar siyo manhajar kidiyar kan kudi naira biliyan 2.8."
Wannan shine kidayar da za a yi bayan shekaru 17 a kasar.
Daily Trust ta rahoto cewa wani ma'aikacin hukumar NPC, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da dage fara aikin kidayar.
Ya ce:
"Yanzu za a fara aikin kidayar daga ranar 3 zuwa 7 na watan Mayu kuma shine abin da aka mika wa Shugaban Kasa. Zai amince da hakan amma bai riga ya sa hannu ba."
Shugaba Buhari ya rantsar da mutum 7 da ya ba wa mukami
A wani rahoton kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da wasu mutane bakwai da ya sabunta nadinsu a matsayin mambobi na majalisar gudanarwa na hukumar ICPC mai yaki da cin hanci.
Buhari Sallau, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanar da hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta.
Asali: Legit.ng