Allah Ya Yiwa Na'ibin Limamin Masallacin Sultan Bello Rasuwa
- Allah ya yiwa mataimakin limamin masallacin Sultan Bello Kaduna, Mallam Ibrahim Isa, rasuwa
- Marigayin ya rasu ne da safiyar ranar Laraba a wani asibiti a cikin birnin Kaduna, bayan rashin lafiya
- Kwamitin masallacin ya bayyana cewa za a yi masa sallar Jana'iza a harabar masallacin bayan an gudanar da Sallar Azahar
Jihar Kaduna- Mataimakin limamin masallacin Sultan Bello dake Kaduna, Mallam Ibrahim Isa, ya rigamu gidan gaskiya.
Allah ya yiwa Mallam Ibrahim Isa Rasuwa ne da safiyar ranar Laraba a asibitin Garkuwa dake cikin birnin Kaduna, bayan yayi fama da rashin lafiya. Rahoton Daily Trust.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamitin masallacin Sultan Bello na Kaduna, ya sanar a shafin sa na Facebook cewa za a gudanar da sallar Jana'izar mamacin ne bayan sallar Azahar a harabar masallacin na Sultan Bello.
Sanarwar na cewa:
“Tare da yarda da ƙaddarar Allah maɗaukakin Sarki, muna sanar da rasuwar mataimakin limamin mu, Mallam Ibrahim Isa, wanda ya rasu yau (Laraba) da safe a asibitin Garkuwa."
“Za a gudanar da Sallar Jana'izar sa a harabar masallacin bayan Sallar Azahar. Allah Ubangiji yayi masa rahama ya sanya Aljannah Firdausi ta zama makoma a gare sa."
Ko a baya an yi babban rashi a Kaduna
Ko a cikin ƴan kwanakin nan da suka gabata an yi wani babban rashi a jihar Kaduna.
Mahaifiyar sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ta rasu. Mahaifiyar malamin addinin musuluncin ta rasu ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairun 2023 a wani asibiti a birnin tarayya Abuja.
An gudanar da jana'izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada a ranar Litinin 6 ga watan Fabrairun 2023, a cikin birnin Kaduna.
Sheikh Ahmed Abubakar Gumi dai yana gudanar da karatuttukan sa a masallacin Sultan Bello dake Kaduna.
Malaman Musulunci Sun ba Tinubu, Zababbun Shugabanni Shawara Kafin Shiga Ofis
A wani labarin na daban kuma, malaman addini da dama sun janyo hankali zaɓaɓɓun shugabanni a ƙasar nan.
Cibiyar addinin musulunci ta ICICE, itace ta shirya wata lakca ta musamman domin janyo hankalin zaɓaɓɓun shugaban kan nauyin da ya rataya a wuyan su na al'umma.
Asali: Legit.ng