Pantami: An yi Yunkurin yi wa Najeriya Kutse Kusan Sau Miliyan 13 Lokacin Zaben 2023
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce sau 12,988,978 aka yi yunkurin yi wa shafukan yanar gizo kutse
- Gwamnatin Tarayya ta ce an kawo hare-haren nan ne yayin da ake yin zaben Shugaban Kasa da Majalisa
- A ranar 25 ga watan Fubrairu, Hukumar INEC ta shirya zaben Shugaban kasa, Sanatoci da 'Yan Majalisa
Abuja - A ranar 25 ga watan Fubrairu 2023, aka yi zaben sabon Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya, gwamnati ta ce an fuskanci barazana iri-iri.
Gwamnatin tarayya ta ce an yi kokarin yi wa shafukan yanar gizon Najeriya kutse sau 12,988,978 a lokacin da Hukumar INEC ta ke shirya zaben shugabanni.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya fitar da jawabi a shafinsa, ya na bayyana haka a ranar Talatar nan.
Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti na musamman da zai bada kariya a shafukan yanar gizo da kuma na’urorin zamani na ICT yayin da ake zabe.
Masu kutse sun karu lokacin zabe
The Cable ta kawo rahoto cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce kafin lokacin zaben nan na bana, kimanin kutse 1,550,000 ake fuskanta a kowace rana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da babban zabe ya zo, lamarin ya munana domin sai da aka fuskanci hare-hare kusan miliyan 13. Ministan ya ce abin ya karu da miliyan shida a ranar zabe.
"A lokacin nan, an fuskanci hare-haren kutse da suka hada da DDoS mai hana shiga shafi, kutsen imel da na IPS, kutsen shiga na’ura SSH, Ppth da sauransu.
Abin lura a nan shi ne cibiyoyinmu sun yi nasarar toshe hare-hare 12,988,978 daga gida da wajen Najeriya, sai aka mika su ga hukuma domin daukar mataki.”
- Farfesa Isa Ali Pantami
Masu ruwa da tsaki sun yi kokari
Rahoton PM News ya nuna Ministan tarayyan ya yabi wadanda suka taimaka wajen samun nasara.
A jawabin da ya fitar, Pantami ya ce masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa da fasahohin zamani sun bada gudumuwa wajen gagarumar nasarar da aka samu.
Ministan ya ce ma’aikatarsa ta kafa kwamitin yakar irin wannan ta’adi ana gobe zabe, a ranar 28 ga watan Fubrairun 2023, wannan kwamiti ya kare aikinsa.
Asarar N20tr a 'yan kwanaki
An ji labari Darektan CPPE yana cewa mutane su na wayyo Allah a dalilin canza N200, N500 da N1000 domin an janye fiye da 70% na kudin da suke yawo.
Dr. Muda Yusuf ya ce Naira Tiriliyan 20 aka rasa da bankin CBN ya yi kokarin canza kudi, hakan ya jawo talauci ya dada yi wa miliyoyin mutane daurin goro.
Asali: Legit.ng