DSS Ta Kama Direkta A Abia Bisa Zargin Barazanar Zai Kashe Masu Zabe

DSS Ta Kama Direkta A Abia Bisa Zargin Barazanar Zai Kashe Masu Zabe

  • Tony Otuonye, daraktan hukumar tallace-tallace ta Jihar Abia ya shiga hannun jami'an DSS bisa barazanar kashe masu zabe
  • Otuonye ya yi ikirarin kashe duk wani wanda ya ki zabar jam'iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Abia ranar Asabar mai zuwa
  • A cikin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya shaida cewa duk wanda zai kawo tsaiko ga nasarar Ahiwe na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, to zai kashe shi

Abia - Hukumar tsaron farin kaya ta kama daraktan hukumar tallace tallace ta Jihar Abia, Tony Otuonye, bisa zargin barazanar kashe duk wanda ya ki zabar jam'iyyar PDP a Abia da dan takarar gwamnanta, Chief Okey Ahiwe, a zaben gwamnoni da za a gudanar Asabar mai zuwa.

Otuonye, a wani bidiyon yakin neman zabe da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya harzuka masu zabe da dama a Abia wanda suke da burin kada kuri'a, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zaben Gwamna: APC Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al'ummar Wata Jihar Kudu

Jami'an DSS
DSS ta kama shugaban hukumar gwamnatin Abia kan yi wa mazu zabe barazana. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ruwaito cewa jami'an farin kaya sun kama shi, kuma ana ci gaba da neman abokan aikinsa.

A bidiyon, Otuonye ya ce zai kashe duk wanda zai kawo tsaiko ga nasarar Ahiwe na jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Jihar.

Jam'iyyar PDP ta nesanta kanta da abin da Otuonye ya aikata

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ta PDP ta nesanta kanta da Otuonye, tana mai cewa ba shi da izini daga jam'iyyar na tada rikici ko yi wa wani barazana.

Mukadashin sakataren watsa labarai na PDP, Abraham Amah, cikin wata sanarwa, ya musanta cewa jam'iyyar na shirin tada rikici yayin zabe, ya ce jam'iyyar ta masu son zaman lafiya ne.

Shugaban DSS na Abia ya ce an bada belin Otuonye

Direktan DSS ya fada wa wakilin Vanguard cewa an kama shugaban na ABSAA a ranar Litinin, an masa tambayoyi kan abin da ya aikata.

Kara karanta wannan

Da Zafi-Zafi: Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili

Ya ce:

"Eh, mun kama shi, mun masa tambayoyi kuma mun bashi beli. Yana asassa rikici."

Da aka masa tambaya ko za a hukunta shi, shugaban na DSS ya ce ba a sallami wanda ake zargin ba.

"Belin ba ya nufin an wanke shi. Zai rika zuwa ofishin mu duk safe yayi zaben."

Shugaban na DSS ya gargadi ya siyasa da magoya bayansu kan aikata duk wani abu da ka iya tada zaune tsaye a jihar.

Ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta sassautawa duk wani da aka samu yana neman jefa jihar cikin rikici ba.

DSS ta kama wasu manyan yan PDP uku a Kaduna kan zargin 'shirin tada tarzoma' yayin zabe da ke tafe

A wani rahoton, jami'an DSS sun cafke mataimakin shugaban kwamitin kamfe din dan takarar gwamna a Kaduna karkashin PDP, Sa'idu Adamu.

An cafke shi tare a El-Abbas Muhammed da Talib Muhammed, shugabannin matasan PDP kan zargin shirin tada rikici lokacin zaben gwamna da yan majalisu da ke tafe a ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Kwankwaso Ya Karbi Bakuncin Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164