'Yan Bindiga Sun Sace Dan Takarar Majalisad Dokoki a Jihar Ribas Gabanin Zabe
- Wani laabri mara dadi da muke samu ya bayyana cewa, an sace dan takarar majalisar dokokin jihar Ribas
- Saura kwanaki uku kacal a yi zaben 'yan majalisun jiha da gwamnoni a Najeriya, amma aka sace jigon jam'iyyar Accord
- Ya zuwa yanzu, wani dangin kusa ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai da sanyin safiyar ranar Talata
Jihar Ribas - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sace dan takarar majalisar dokokin jiha a mazabar Ogba/Egbema/Ndoni 2 a jihar Ribas, Chukwudi Ogbonna.
Dan takarar na jam’iyyar Accord ya shiga hannun ‘yan bindigan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a Najeriya.
An ce an sace Mr. Ogbonna ne a Rumuigbo da ke kusa da Fatakwal a ranar Litinin da dare yayin da yake tuka motarsa.
Kisan Kai: Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Majalisar Tarayya Na Birni a Arewa Ruwa a Jallo, Sun Sa Lada N1m
Dan uwan dan takaran, wani Ifeaka Nwakiri ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch a ranar Talata 14 ga watan Maris da safe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Sun sace shi tare da motarsa Mercedes. Mun kai rahoton batun ga ofishin ‘yan sanda da ke Kala.”
Akwai siyasa a lamarin nan
Nwakiri ya yi zargin cewa, sace dan uwan nasa na da alaka ta kusa da lamarin da ya shafi siyasa, inda ya yi ga ‘yan sanda da su dauki mataki.
Hakazalika, ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta dage zaben ranar Asabar a yankin har sai an sako dan uwansa da ke takara, rahoton Daily Post.
A cewarsa:
“Rokonmu da kiranmu shine gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kwamishinan ‘yan sanda, daraktan DSS, NSCDC duk su hobbasa don tabbatar da an ceto Injiniya Chukwudi Ogbonna.”
An lallasa wadanda ke son dagula zabe a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar tsaro ta yi nasarar fatattakar wasu ‘yan ta’addan da suka so tada hankalin jama’a a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Rundunar sojin ta bayyana yadda ta yiwa ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas babu dadi a jajiberin zaben shugaban kasa.
Hakazalika, rundunar ta ce ta lallasa wasu tsagerun da suka yi kokarin kawo tsaiko ga zaman lafiyar zabe a jihar Kogi da Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Asali: Legit.ng