Gidan Man Gwamnan Ogun Ya Ki Karbar Tsoffin Naira Duk da Barazanar da Yake Yiwa ’Yan Kasuwa

Gidan Man Gwamnan Ogun Ya Ki Karbar Tsoffin Naira Duk da Barazanar da Yake Yiwa ’Yan Kasuwa

  • An samu rudani yayin da gidan mai mallakin gwamnan APC ya daina karbar tsoffin kudi duk da gargadin da gwamnan ya yi na hukunta masu irin wannan laifin
  • Masu ababen hawa sun shiga damuwa na yadda rashin karbar tsoffin kudin ke shafarsu, daya daga ciki ya bayyana kokensa
  • Gwamna Abiodun na jihar Ogun ya sha bayyana matsayarsa na hukunta duk wanda ya ki karbar tsohon kudi, amma gidan mansa ba a karba

Jihar Ogun - A wani bidiyo da jaridar Premium Times tace ta samo, an ga ma’aikacin gidan mai mallakin gwamna Dapo Abiodun ya ki karbar tsoffin N500 da N1000 duk da gargadin da gwamnan ya yi na hukunta masu kin tsohon kudi.

Abiodun a baya ya yi gargadin cewa, zai garkame dukkan kantuna, bankuna da shagunan siyayya da ke kin karbar tsoffin kudi bayan umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Rikicin Naira: Masu gidajen mai sun ki karbar tsoffin kudi duk da umarnin CBN, sun fadi dalili

Gwamnan ya yi kira ga mazauna jiharsa da su kai rahoton duk wanda yaki karbar tsohon kudi daga hannunsu, zai tabbatar da rufe wurin kasuwancin.

Ba a karbar tsohon kudi a gidan man gwamna
Yadda lamarin sabbin kudi ke jan hankali a Najeriya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

A watan Faburairu yayin da yake kamfen a Abeokuta North ta jiharsa, ya ziyarci kasuwar Kampala a Itoku, inda ya shaidawa ‘yan kasuwan cewa, zai rufe shagon duk wanda ya ki karbar tsohon kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau, yayin da yake magana da magoya bayansa a wani bidiyon, gwamnan ya sake jaddada matsayarsa kan wannan batu na kin tsoffin kudi.

An samu rudani, gidan man gwamna ba ya karbar tsohon kudi

Amma a sabon bidiyon da aka gani na gidan mai mallakin gwamnan, an ga lokacin da ake fada wa masu siyan mai cewa, tsoffin kudi ba za su samu shiga ba.

Wani mai abin hawa da ya yi magana ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna APC Ya Faɗi Muhimmiyar Maganar da Ya Yi da Gwamnan CBN Kan Sauya Naira

“Meye yasa ba za ku karbi tsoffin kudin ba? Gwamna ya ba da umarnin dukkan ‘yan kasuwa su karbi tsoffin kudi ko wannan ba gidan man gwamnan bane? Ba damuwa, na gode.”

An yi kokarin jin ta bakin sakataren yada labarai na gwamnan, Kunle Shomorin, amma ba a yi nasara ba domin bai amsa waya ba kuma bai dawo da sakon tes da aka tura masa ba.

Masu gidajen mai sun ki karbar tsoffin Naira

A bangare guda, masu gidajen mai sun ce ba za su ci gaba da karbar tsoffin kudi ba har sai an cika wata ka’ida guda daya.

A cewarsu, duk da umarnin CBN, ba za su ci gaba da karbar kudin ba har sai sun ga bankunan kasar sun fara karbar kudin gada-gadan.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da CBN ya ce ya bi umarnin kotun koli na ci gaba da karbar tsoffin Naira har karshen Disamba.

Kara karanta wannan

“Kudi Da Nake Nema” Matashi Ya Yi Bidiyon Buhuhunan Tsoffin Kudi Da CBN Ya Nika Ya Watsar

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.