Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Ne Saboda Shi Kadai Ne Dan Takara Karbabbe a Najeriya
- Jigon jam’iyyar APC ya bayyana kadan daga dalilan da yasa Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya a watan jiya
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan adawa ke cewa, an yi murdiya a zaben an ba Tinubu mulki alhalin bai lashe zabe ba
- A bangare guda, ya ce Tinubu ne ya fi karbuwa a kowane yanki a kasar nan sabanin sauran ‘yan takarar shugaban kasa
FCT, Abuja - Festus Kayemo, kakakin tawagar gangamin APC a matakin shugaban kasa ya ce, zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya lashe zabe ne saboda shi kadai ne dan takarar da ya kasance mai kishin Najeriya kuma karbabbe.
Kayemo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na TVC wanda Legit.ng Hausa ta sanya ido a kai.
Idan baku manta ba, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan ya samu kuri’u sama da miliyan 8.
Nasarar Tinubu ta jawo cece-kuce daga jam’iyyun adawa, inda Atiku Abubakar na PDP, wanda ya zo na biyu a zaben da kuma Peter Obi na Labour da ya zo na uku suka tsaya tsayin daka sai sun kalubalanci sakamakon a gaban kotu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ne karbabben dan takara a Najeriya
Sai dai, da yake martani ga sakamakon zaben, Kayemo ya ce, dan takarar na APC ya samu kuri’u ne saboda samun goyon bayan da yake dashi daga bangarori daban-daban na Najeriya.
A cewarsa:
“Tinubu ne dan takarar da ke da kuri’u a ko ina a Najeriya kuma ya samu kuri’u daga yankuna da shiyyoyi mabambanta.
“Wanda ya lashe zaben, Tinubu, ya samu goyon baya daga ko ina a Najeriya – daga Arewa, Kudu, Gabas, da Yamma.
“Yana da kuri’u daga kowane yanki a Najeriya. A bayyane yake duba da tsarin zaben, ya kuma nuna sakamakon yadda sauran ‘yan takara suka yi kamfen dinsu.”
Ba Tinubu bane zabin Allah, inji Obi
A wani labarin kuma, kunji yadda dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana cewa, ba Tinubu bane Allah ya zabarwa ‘yan Najeriya.
Dan takarar na Labour ya bayyana cewa, bai kamata a yi amfani da sunan Allah wajen aikin rashin gaskiya da murdiya ba.
A tun farko ya bayyana yadda zai kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a kasar saboda wasu dalilai.
Asali: Legit.ng