Tsofaffin Kudi: Gwamnoni Sun Kuma Yin Taron Dangi, Sun Ba Gwamnatin Buhari Wa’adi

Tsofaffin Kudi: Gwamnoni Sun Kuma Yin Taron Dangi, Sun Ba Gwamnatin Buhari Wa’adi

  • Gwamnatocin Jihohi za su iya komawa kotu idan aka ki dawo da tsofaffin ‘Yan N500 da N1000
  • Lauyoyin Jihohin da suka je kotun koli sun nuna shirya yin karar Ministan shari’a da Gwamnan CBN
  • Litinin ce ranar karshe da idan ba a bi umarnin Alkalai ba, za ayi shari’a tsakanin jihohi da tarayya

Abuja - Gwamnonin jihohin da suka kai gwamnatin tarayya kara a kotun koli, sun bukaci bankin CBN da AGF da su yi wa hukuncin kotu biyayya.

A wani dogon rahoto na Punch, an fahimci gwamnonin sun yi barazanar shigar da karar Godwin Emefiele da kuma Abubakar Malami SAN a kotu.

Idan aka kai ranar Talata ba tare da Gwamnan babban banki da Ministan shari’a sun bi umarni ba, jihohin za su zarge su da yi wa kotu rashin kunya.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zaben Gwamna: APC Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al'ummar Wata Jihar Kudu

Rahoton ya ce Kwamishinan shari’a na jihar Zamfara, Junaidu Aminu ya ce za su koma kotu domin tabbatar da an yi abin da Alkalai suka zartar.

Jihar Zamfara za ta dauki mataki

Junaidu Aminu ya ce sun gabatar da takardun CTC ga babban Lauyan gwamnatin tarayya, su na masu sa ran gwamnati za ta yi biyayya ga kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan na jihar Zamfara yake cewa dole ne Gwamnan CBN ya fito ya yi wa jama’a jawabi.

Buhari
Gwamnan babban banki da Shugaba Buhari Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Facebook

"Mu na sauraron su yi biyayya ga umarnin kotun koli a kan batun tsofaffin kudi. Idan ba su bi umarnin a ranar Litinin ba, Talata za mu shigar da kara.
Dole Emefiele ya yi wa ‘Yan Najeriya jawabi a kan tsofaffin kudi akalla zuwa yau (Litinin), la’akari da cewa abin da mutane suke tsammani kenan.
Idan ya gagara yin haka, za mu sake komawa kotu, muyi kararsa da gwamnati a kan rashin kunya."

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Gwamnoni Ba Su Hakura ba, Za Su Sake Kai Karar Gwamnatin Buhari a Kotu

- Junaidu Aminu

Menene laifin AGF?

Lauyan yake cewa a matsayinsa na Ministan shari’a, Abubakar Malami ne zai umarci gwamnan CBN da ya bi umarnin Alkalan kotun kolin kasar.

Kwamishinan shari’a na Kuros Ribas, Tanko Ashang ya ce a shirye suke su hadu wajen shigar da karar, wannan shi ne ra’ayin gwamnatin jihar Kogi.

Kingsley Fanwo ya shaidawa manema labarai cewa sun fara kokarin tabbatar da an bi umarnin. Dayo Apata, SAN ya ce Ekiti ta na tare da sauran jihohi.

AGF da CBN sun yi gum

An ji labari Lauyan da ya tsayawa Kaduna, Kogi and Zamfara, Abdulhakeem Mustapha (SAN), ya ce kotu ta ba AGF takardun shari’ar da suka yi.

Sama da mako guda kenan da kotun koli tayi umarni da a cigaba da amfani da tsofaffin N500 da N1000, amma har yanzu gwamnati ba tace uffan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng