Hotunan Kashim Shettima Lokacin da Yake Dalibin Jami’a Sun Jawo Cece-Kuce a Twitter

Hotunan Kashim Shettima Lokacin da Yake Dalibin Jami’a Sun Jawo Cece-Kuce a Twitter

  • Kashim Shettima ya ba da mamaki yayin da ya yada hotunansa na lokacin da yake karatu a jami’ar Maiduguri da ke Borno
  • Jama’ar kafar sada zumunta sun tashi da tambayar cewa, meye yasa zababben mataimakin shugaban kasan ba ya dariya
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da cece-kuce a Najeriya bayan da aka alanta Tinubu da Shettima a matsayin wadanda suka lashe zaben shugaban kasa

Najeriya - Zababben mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Kashim Shettima ya yada hotunansa na lokacin da yake karatu a jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

A hotuna guda biyu da ya yada, an ga Shettima a tsaye a daya hotun shi kadai, yayin da daya kuma aka ganshi tare da abokinsa na karatu a wancan lokacin.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi ta cece-kuce tare da yin martani mai daukar hankali kan wadannan hotuna masu cike da tarihi.

Kara karanta wannan

Toh fa: An sanyawa masallaci sunan gwamna Kirista, kungiyar Musulmai ta yi martani

Hotunan Shettima sadda yake dalibin jami'a
Wannan Shettima kenan a sadda yake dalibin jami'a | Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

A lokacin da jaridar Vanguard ta sake yada hotunan a Twitter, mutane sun yi mamakin yadda suka ga mataimakin shugaban kasan ba ya dariya a hotunan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli hotunan:

Martanin da jama’a ke yi

Legit.ng Hausa ta yi duba ga abin da mutane ke cewa bayan ganin hotunan, ga kadan daga abin da muka tattaro muku.

@ojoteosas:

“Ina jiran ganin yaushe Tinubu zai yada hotunansa na makaranta.”

@OscarChinaemer1:

“Yaushe Tinubu zai yada hotunan tuna baya na lokacin da yake makaranta.”

@topboiy1:

“Ba ya dariya.”

@ladkings:

“Yaushe ne zai samu farin ciki?”

@Rahmer_LG:

“Waye ne a kusa dashi?”
@Chambers3383:
“Shin zababben shugaban kasa ma zai iya yin haka...?
“Tambaya kawai nake, bari na gudu kafin wani ya kira DSS din da ke Twitter.”

Yarbawa sun tubure, sun ce ba Tinubu bane ya lashe zaben shugaban kasa na bana ba

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

A wani labarin, kunji yadda Yarbawa a suka bayyana rashin amincewarsu ga nasarar Bola Ahmad Tinubu duk da kuwa ya fi kowa yawan kuri'u.

Kungiyar Afenifere ta ce, tabbas Peter Obi ne ya lashe zaben bana, amma INEC ta dauki dansu Bayarbe ta bashi.

Obi da Atiku sun bayyana rashin amincewa da sakamakon zabe, sun ce za su kalubalanci lamarin a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.