MURIC Ta Tada Hankali Bayan da Aka Sanyawa Masallaci Sunan Gwamna Kirista a Jihar Oyo

MURIC Ta Tada Hankali Bayan da Aka Sanyawa Masallaci Sunan Gwamna Kirista a Jihar Oyo

  • MURIC ta dauki zafi yayin da ta samu labarin sanyawa masallaci sunan gwamna kirista saboda dalili daya a jihar Oyo
  • Kungiyar ta zargi gwama addini da siyasa, da kuma raina addinin al’ummar Musulmin jihar ta Oyo da ke Kudancin Najeriya
  • Kungiyar ta MURIC ta bayyana abin da take so a gaggauta yi don kwantar da hankalin Muslmai a jihar Oyo

Jihar Oyo - Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta bayyana rashin jin dadinta ga shawarin da gwamnatin Oyo ta yi na sauya sunan babban masallacin da ke Iwo Road a Ibadan zuwa sunan gwamna Seyi Makinde.

Kungiyar ta addinin Islama ta kuma bukaci da a gaggauta mayar da tsohon sunan masallacin ba tare da bata lokaci ba.

MURIC ta bayyana wannan batu ne ta bakin Daraktanta, Ishaq Akintola, kamar yadda ya wallafa a shafin kungiyar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Shaguna sun kone a wata fitacciyar kasuwar Kano, kauyuka 3 sun kone a Jigawa

An sanyawa masallaci sunan gwamna kirista a Najeriya
Masallacin da MURIC ta nemi a sauyawa suna | Hoto: freshpage.com.ng
Asali: UGC

Yadda lamarin ya fara a tun farko

A wata Juma’a a watan Oktoban 2019, gwamna Makinde ya sanar da rushewa tare da sake gina babban masallacin Adogba a wani wuri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya ce, za a kammala aikin sake gina masallacin ne cikin watanni tara zuwa 11, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, cocin da ke yankin shima za a rushe shi tare da yin sabo.

Ya zuwa yanzu dai an sake gina masallacin a wani wurin shekaru kusan hudu bayan da gwamnan ya yi alkawari.

Abubuwan da aka saka a cikin masallacin

A cikin masallacin, akwai makarantar Islamiyya, cibiyar nazarin addini, dakin karatu, dakin taro da kuma katafaren filin ajiye ababen hawa.

Ta haka ne aka maka sunan gwamnan, inda MURIC ta bayyana rashin dadinta da cewa, gwamnan na son amfani da damar ne don cimma manufar siyasa.

Kara karanta wannan

Nwosu: Za a Fara Zaman Makoki a APC, Shugaba a Jam’iyya Ya Rasu a Asibiti

A cewar MURIC:

“Ko da lokacin kammala aikin ma sai da aka lissafa shi ya yi daidai da lokacin zaben 2023. Seyi Makinde ya yi wasa da hankalin al’ummar Musulmin jihar Oyo ne.”

Kungiyar ta kuma siffanta sanyawa masallacin sunan gwamnan a matsayin raina addini da wurin ibada, kasancewar Makinde kirista ne.

A kasar Turai, ta Ukraine, an samu wani mutumin da ya musulunta bayan da ya samu mafaka a wani masallaci a lokacin da yaki ya barke a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.