Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli'

Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli'

  • A yayin da mutanen Najeriya ke fama da karancin kudi, jami'an hukumar tsaro ta NSCDC sun kama wasu mutane da jabun naira da daloli
  • Olusola Odumosu, direktan sashin hulda da jama'a na NSCDC ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri kansu
  • Wadanda aka kama din sun amsa cewa suna harkar sarrafa jabun kudaden kuma ana cigaba da zurfafa bincike don kamo sauran abokansu

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce ta kama mambobin wata tawaga da aka ce suna sarrafa tare da raba jabun dalolin Amurka da sabbin takardun naira, rahoton The Cable.

Yayin hirarsa da kamfanin dillancin labarai NAN ranar Juma'a a Abuja, Olusola Odumosu, jami'in hulda da al'umma na hukumar ya ce an kama wadanda ake zargin ne a jihar Filato tsakanin 22 ga watan Fabrairu zuwa 8 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Yaudari Kwararriyar Yar Gidan Magajiya Ya Tura Mata Alat Din N120,000 Na Bogi Bayan Gama 'Harka'

Jami'an NSCDC
An kama wasu da jabun daloli da takardun naira. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Odumosu ya ce mambobin daya cikin tawagar, sun kunshi maza hudu, an kama su ne dauke da dallar Amurka na bogi 64,800 da N475,000.

Ya kuma ce an kwato jabun kudi har naira miliyan 1.5 daga hannun tawagar ta biyu da ta kunshi maza biyar.

Ya ce:

"Daga cikin N1.5m da aka kwace, N784,500 na bogi ne yayin da N49,650 tsaffin naira ne."

Yadda aka kama wadanda ake zargin

Ya ce an kama tawagar ta farko ne bayan samun bayanan sirri cewa suna kan hanyarsu na zuwa kai wa wani abokin harkarsu kudin jabu a jihar Nasarawa.

Odumosu ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu kan abin da ake zargin suna yi, yana mai cewa rundunar na zurfafa bincike kuma tana farautar sauran mambobin tawagar.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Ya ce binciken da suke yi ya nuna tawagar ta yi aiki a jihohin Nasarawa, Filato, Bauchi, da Gombe na tsawon shekaru kafin asirinsu ya tonu.

Amoketun sun kama wani mutum dauke da tsabbar sabbin kudi N250,000 na bogi

A wani labarin mai kama da wannan, jami'an hukumar tsaro na kudu maso yamma wato Amotekun sun kama wani mutum, Celestine da takardun naira na bogi da adadin su ya kai N250,000.

Hakan na zuwa ne a lokacin da mutanen Najeriya ke fama da karancin kudaden a sassa daban-daban

Wanda aka kama din, Celestine, ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa ne kuma haifafan Anambra amma yana zaune a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164