'Yan Siyasa Sun Karbi Lambobin Asusunmu Amma Sun Ki Tura Ko Kobo, Masu Kada Kuri’u a Neja Sun Koka
- Mazauna a jihar Neja sun bayyana kokensu kan yadda ‘yan siyasa suka yaudare su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya
- Alamu sun nuna cewa, an ba wasu masu kada kuri’u kudaden kasar waje domin siyan kuri’unsu a zaben da ya wakana
- Jami’in dan sanda da lauya sun yi bayani, sun ce siya da siyar da kuri’u babban laifin ne a dokar Najeriya, ya kamata jama’a su kula
Jihar Neja - Wasu mutanen jihar Neja sun zargi ‘yan siyasa da yaudararsu ta hanyar karbar lambobin asusun bankinsu gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, amma sun ji shuru.
Mrs Felicia Sunday ta shaidawa City & Crime cewa, jam’iyyun siyasa da yawa ne suka karbi lambobin asusunsu makwannii biyu kafin zaben, amma har yanzu ba a tura musu ko kobo kamar yadda aka yi musu alkawari.
Idan baku manta ba, gwamnati ta ce ta kawo batun sauyin kudi ne domin rage yawaitar siyan kuri’u a lokacin zaben 2023.
‘Yan siyasa sun iya yaudara
Da take bayyana kokenta kan rashin ba su ko kobo bayan alkawarin, Felicia ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Sun karbi lambobin asusunmu a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya amma har yanzu bamu ji komai ba. Wasu har da yi mana alkawarin N5,000.
“Wadannan ‘yan siyasan mayaudare ne. Ba zan sake yarda da su ba.”
Sai dai, ta bayyana cewa, wasu jam’iyyun siyasan sun yi rabon kayan abinci garesu, kamar dai shinkafa, taliya, Maggi da gishiri.
Malam Danjuma Muhammad, wani mazaunin jihar ta Neja shi ma ya ba da irin wannan labari ga jaridar Daily Trust, inda yace an karbi lambar asusunsa a lokacin zaben.
Sun ce za su ba da N5000, amma shuru, inji wani
Har ila yau, wani Mr. Philip Nma ya ce ya ba da lambar asusunsa ga wani wakilin dan siyasa da sunan za su turo masa N5000, amma bai ji komai ba har yanzu.
Ya bayyana cewa, jama’a sun yi wayo tare da gane yaudarar da ke cikin lamarin, inda suka ce ba za su saurari wani dan siyasa ba a zaben gwamna da ke tafe.
Wani mai sana’ar POS ya shaidawa jaridar cewa, wasu wadanda suka kada kuri’u a zaben shugaban kasa sun zo masa da Dalar Amurka domin ya siya bayan zaben 25 ga watan Faburairu.
Wannan babban laifi ne, cewar tsohon dan sanda
Mr Sunday Ajeromi, wani tsohon jami’in dan sanda ya shaida cewa, babban laifi ne jama’a su karbi kudi domin su dangwala kuri’arsu a zabe.
Ya bayyana cewa, dokar kasa ta tanadi bayanai cewa, duk mai siyar da kuri’u ko siya ya sani hakan ta’addanci ne mai girma.
Ya ce, a madadin koken da suke yi, kamata ya yi ma hukumomin tsaro su kama su tare da gurfanar dasu a kotun da ya dace.
Isa Usman Esq, wani lauya mai zaman kansa a jihar Kaduna ya zanta da wakilin Legit.ng Hausa kan tanadin doka game da siya da siyar da kuri'u.
Ya ce:
"Sabuwar dokar zabe da shugaba Buhari ya sanyawa hannu ta ayyana musayar kuri'u da kudi a matsayin aikin ta'addanci.
"Ya kamata mutane su gane, idan ka siyar da kuri'arka, ka yi laifi, idan ka siya, shi ma laifi ne."
Asali: Legit.ng