‘Ba Dai Ni Ba’: Jama’a Sun Girgiza Bayan Ganin Budurwa a Kan Giwa Tana Daukar Hoto

‘Ba Dai Ni Ba’: Jama’a Sun Girgiza Bayan Ganin Budurwa a Kan Giwa Tana Daukar Hoto

  • Alakar wata budurwa da wata kafceciyar giwa ya ba da mamaki a kafar sada zumunta ta bidiyo, wato TikTok
  • A bidiyon da aka yada a TikTok, an ga budurwar na kan wata giwa, ta hau ta dare ta zauna dabas kamar wacce ta hau doki
  • Giwar ce da kanta ta tallafawa matar ta hau saman bayanta, lamarin da ya ja hankali a kafar sada zumunta na TikTok

A wani bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da wata mata ke darewa kan makekiyar giwa kamar wacce ta samu doki.

A bidiyon da @chalidahomniem ya yada, an ga matar a tsakiyar wasu manyan giwaye guda biyu kamar ba abin tsoro ba.

Daga alakar da ke tsakaninsu, ‘yan TikTok sun yanke cewa, matar da giwar ba za su rasa nasaba ta abota ba a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

"Na Shiga Uku": Wani Dan Najeriya Ya Koka Bayan Gayyatar Wata Budurwa Ta Kwana A Gidansa, Ya Wallafa Bidiyo

Yadda wata ta yiwa giwa hawan doki
Hotunan lokacin da take hawa kan giwa | Hoto: @chalidahomniem
Asali: TikTok

Bidiyon budurwar da ta hau giwa

A gajeren bidiyon da aka yada, an ya matar na lallabawa tana taba kunnuwan giwa da kafarya daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A nata bangaren, giwar ta sunkuwar da kafarta daya don matar ta samu damar hawa samanta.

Yayin da ta hau saman giwar, sai ta nuna alamar cin nasarar hawa saman giwa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Bidiyon ya jawo cece-kuce a TikTok, ga kadan daga abin da suke cewa:

@user8242385816395:

"Ina son wannan."

@lawangarba687:

"Wannan ba zai taba kasancewa ni ba."

@abdu44:

"Fatan alheri."

@Finbarr Gini Sarki:

"Yi tunanin alakar sadarwa tsakanin dan adam da dabba.”

@Green fingers:

"Ta yaya za ki sauko kasa.”

@HAMARACK:

"Kai ina son wannan gaskiya.”

Mutum ya ga kafcecen kifi a bakin teku, ya mai dashi ruwa

Kara karanta wannan

“Muna Alfahari Da Ke”: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo a Kan Murhu Kamar Babba Ya Girgiza Intanet

A wani labarin mai kama da wannan, kun ji yadda wani mutum ya dauko kifin da ya gani a ruwa, ya mai dashi cikin teku ba tare da cutar dashi ba ko kuntata masa.

Bidiyon da muka samo ya nuna lokacin da mutumin ya kama kifin cikin tsanaki tare da tallafa masa ya shiga ruwa cikin yanayi na tausayawa da kaunar dabba.

Mutane da yawa sun bayyana martaninsu mai daukar hankali da ganin wannan bidiyo mai cike da ban mamaki da taba zuciya, sun ce ya yi kokari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel