‘Ba Ka da Tukunya Ne’: Martanin Jama’a Bayan da Wani Ya Mai da Kifi Ruwa Bayan Kama Shi

‘Ba Ka da Tukunya Ne’: Martanin Jama’a Bayan da Wani Ya Mai da Kifi Ruwa Bayan Kama Shi

  • Akalla mutum miliyan 3 ne suka kalli bidiyon wani mutum mai tausayi da ya ga katon kifi a bakin teku kana ya maida shi ruwa
  • A bidiyon da ya yi shuhura a TikTok, mutumin ya ga kifin ne ya fito bakin ruwa amma ya gaza komawa, sai ya taimake shi cikin sauki
  • Bai tsaya wata-wata ba ya gaggauta kama kifin ta wutsiya tare da tura shi cikin ruwa a hankali, lamarin da ya ja hankalin jama’a

Wani mutumin da ya kama katon kifi ya sake shi ya koma cikin ruwa ba tare da cutar dashi ba a cikin wani bidiyo ya jawo cece-kuce.

A bidiyon da aka yada mai yawan dakiku 41 a kafar TikTok, an ga lokacin da mutumin ke tafiya a bakin ruwa har ya ga kifin.

Kara karanta wannan

An Kashe Mutane 50, An Raunata Da Dama, An Kona Gidaje Yayin Hare-Hare A Binuwai

A bidiyon, an ga lokacin da kifin ya fito bakin ruwa yana kwance a cikin kasar bakin teku, ya gaza komawa cikin ruwa.

Yadda wani ya kama katon kifi ya mai dashi ruwa ya jawo cece-kuce
Hoton mutumin da ya kama kifi ya mayar ruwa | Hoto: zahiddubai7
Asali: TikTok

Mutumin ya maida kifi ruwa

Ba a dai san yadda kifin ya fito bakin ruwan ba, amma alamu sun nuna ya gaji, ya gaza komawa ne yana bukatar taimako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin da ya iso wurin, bai yi wata-wata ba ya tsaya don taimakawa kifin. Ya kama shi ta wutsiya, kana ya ja shi zuwa cikin ruwan.

Bayan tsoma shi cikin ruwa, cikin dakiku kadan kifin ya ci gaba da shawaginsa a cikin ruwa kamar yadda rayuwarsa take.

Wannan lamari ya dauki hankalin jama’a a kafar TikTok, mutane da yawa sun bayyana martani mai daukar hankali a kai.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’ar TikTok

@Vawulence ITunes:

"A Najeriya, cewa za mu yi Allah ya albarkace mu yau.”

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Baya Ga Dogon Layi a Banki, Kwastomomi Sai Sun Ba Da Cin Hanci Kafin Su Iya Shiga Banki

@Alkebulan:

"Ba ka da tukunya ne?”

@skyark pecky:

"Ka san nawa ne darajar kifin nan kuwa a Najeriya? Haka kawai ka barshi ya tafi.”

@Sharles:

"Yunwa bata kama ka ba gaskiya.”

@FredG:

"Meye wani tausayi? Shin bai jin kwadayin kifi ne?”

@Demilade:

"A nan Najeriya za mu yi farfesu ne dashi.”

A wani labarin kuma, matasa sun kare a kotu bayan da suka karya kofar shiga kantin siyayya na Shoprite a wata jiya, inda aka zarge su da aikata mummunar barna da ba a so ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel