"Ina da cikin wata 5 amma ban sani," Wata Mai Shayarwa A Bidiyo

"Ina da cikin wata 5 amma ban sani," Wata Mai Shayarwa A Bidiyo

  • Wata mai shayarwa da ta ɗauki juna biyu ba ta sani ba, ta bayyana yadda rayuwarta take tafiya cikin walwala
  • A cewarta, yarinyar da take goyo ba ta damu ba yayin da cikin ƙaninta ke kara girma tsawon watanni
  • Matan da ke burin haihuwa nan gaba sun maida mata martani da cewa dole ta karfafa kanta kafin haye wannan yanayin

Wata mata (@meetmykids) a wani bidiyo da ta wallafa a soshiyal midiya, ta labarta yadda ta ɗauki sabon juna biyu yayin da take tsaka da shayarwa.

Matar ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta san ta ɗauki wani cikin ba saboda dama ta daina jinin al'ada bayan ta haihu.

Mata mai shayarwa ta dauki juna biyu.
"Ina da cikin wata 5 amma ban sani," Wata Mai Shayarwa A Bidiyo Hoto: @meetsmykid
Asali: TikTok

Lokacin da ta fahimci jikinta na sauyawa, matar ta yi tunanin ba abun mamaki bane saboda tana shayar da ɗiyarta.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Aure Mahaifin Tsohon Saurayinta Bayan Rabuwa da Shi

Ga goyo ga juna biyu

Watanni biyar da shigar cikin, matar ta ce ba ta kamu da rashin lafiya ba kuma ba ta ga wata alama da zata yi tunanin tana ɗauke da juna biyu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, kyakkyawar matar ta ƙara da bayanin cewa ɗiyarta na girma gunin sha'awa a tsawon lokacin, "Ɓoyayyen juna biyu."

Daga karshe ta yi addu'a tare da fatan Allah ya sauki iyaye matan da suka tsinci kansu a irin wannan yanayin lafiya.

Kalli bidiyon anan

Martanin mutane a soshiyal midiya

Zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoton, sama da mutane 900 sun bayyana ra'ayoyinsu kuma akalla 40,000 suka kalla.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin martanin mutane kamar haka;

Favour Eloben ta ce:

"Ina fatan haka ta faru da ni, ina son ɗaukar ciki kwanan nan, na taya ki murna 'yar uwa."

Kara karanta wannan

Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel.

Maris ta ce:

"Haka na garzaya a mun gwajin juna biyu saboda ban ƙara ganin al'ada ta ba tun lokacin da na haihu, watanni 13 kenan, ina ta ya ki murna."

Baby Bryanne ta ce:

"Muna ɗaya da ke, yarinya 'yar shekara ɗaya a duniya da juna biyu na watanni shida. Abun ba sauki amma kin ƙara mun kwarin guiwa. Ina Addu'a Allah ya bani namiji."

Wani Mutumi Ya Miƙe Daga Kan Keken Guragu, Ya Kama Rawa da Amarya

A wani labarin kuma Wani mutumi da ya halarci shagalin bikin aure a kan Keken Guragu ya bar mutane baki buɗe.

Da zuwan mutumin amarya ta ja shi kan dandamalin rawa, mintuna kaɗan aka ga ya miƙe kan kafafunsa ya kama rawa a wani bidiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262