Ganduje Ya Nada Mai Shari’a Dije Aboki a Matsayin Babbar Alkalin Rikon Kwarya a Kano

Ganduje Ya Nada Mai Shari’a Dije Aboki a Matsayin Babbar Alkalin Rikon Kwarya a Kano

  • Ana dab da zaben da zai sauka a mulki, gwamna Ganduje ya yi sabon nadi a ma’aikatar shari’a ta jihar Kano
  • An nada mai shari’a Dije Aboki a matsayin sabuwar babbar alkalin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Rahoton da muka samo ya bayyana kadan daga tarihin wannan ma’aikaciya kwararriya a fannin da ya shafi shari’a

Jihar Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da nada mai shari’a Dije Aboki a matsayin babbar alkalin rikon kwarya na jihar.

Nada Dije na zuwa ne biyo bayan ajiye aiki da yin ritayan babban alkalin jihar, mai shari’a Nura Sagir, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar a ranar Laraba 8 ga watan Maris ce ta bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

Ganduje ya yi sabon nadi a ma'aikatar shari'a
Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar sanarwar, Dije ta kasance alkali a babban kotun jihar tun shekarar 2006, kusan shekaru 17 kenan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Garba nadin nata ya fara aiki ne daga ranar Larabar da aka fitar sanarwar nada ta, rahoton TVC News.

Wacece mai shari’a Dija?

A cewar sanarwar:

“Aboki ta kasance dalibar ilimin shari’a a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta gama digiri a 1983, ta zama lauya a 1984.
“Aboki ta fara aikin shari’a ne a 1985 a karkashin ma’aikatar shari’a ta jihar. Bayan shekara daya, aka nada ta alkali a kotun Majistare kuma haka ta girma zuwa alkali a babban kotun jiha a 2006.”

Hakazalika, ta kasance mamba a manyan kungiyoyin kwararrun masu aikin shari’a kana ta rike manyan mukamai masu yawa.

Nada wannan kwararriyar ma’aikataciya dai na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki kadan gwamnan Kano ya sauko kasancewar ya kwashe wa’adi biyu yana mulki.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: INEC ta fito da kayan aikin zabe, ta fara raba su a wata jihar Arewa

Ganduje ya yiwa fursumomi afuwa

A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamna Ganduje na jihar Kano ya bayyana yiwa wasu fursunoni 12 da aka yankewa hukuncin kisa afuwa a magarkamar Kano.

Hakazalika, gwamnan ya sauya hukuncin kisan da aka yiwa wasu fursunoni shida zuwa daurin rai-da-rai.

Gwamnan ya kuma yi bayanin dalilin da yasa gwamnoni ba sa son sanya hannu kan hukuncin kisa haka siddan ba tare da dogon nazari da binciken da ya dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.