Yadda Tsohon Hafsun Sojoji Ya Sace N2bn a Asusun Sojan Sama – Shaidan EFCC a Kotu

Yadda Tsohon Hafsun Sojoji Ya Sace N2bn a Asusun Sojan Sama – Shaidan EFCC a Kotu

  • Lauyoyin hukumar EFCC sun kira Okechukwu Akube a matsayin shaida a shari’arsu Adesola Amosu
  • Tsakanin 2014 da 2015, Air Marshall Adesola Amosu shi ne Shugaban hafsun sojojin sama a Najeriya
  • EFCC ta ce Hafsun da wasu tsofaffin jami’ai sun hada-kai sun sace N2bn daga asusun gidan sojoji a 2014

Lagos - A ranar Laraba, hukumar EFCC ta kira wani Okechukwu Akube ya bada shaida a shari’ar da ake yi da su Adesola Amosu a kotun tarayya a Legas.

Punch ta ce Okechukwu Akube ya yi wa Alkali bayanin yadda wadanda ake zargi suka karkatar a Naira Biliyan biyu daga asusun kar-ta-kwana na sojin sama.

Mai bada shaidar ya ce an yi amfani da Biliyoyin wajen mallakar gida a Ikoyi a Legas.

Wannan bayanai sun fito ne a zaman shari’ar Adesola Amosu, Air Vice Marshal Jacob Adigun da Air Commodore Gbadebo Owodunni a kotun da ke Legas.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Amosun da Sojoji 2 sun koma kotu

Ana zargin Amosu wanda ya rike Hafsun sojojin sama da tsohon Akantan gidan sojan, Adigun da kuma tsohon Darektan kudi, Owodunni da satar N21bn.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyoyin EFCC su na kokarin gamsar da Kotu wadannan tsofaffin sojoji uku sun sace kudin tsaro, sun jefa a cikin aljihunansu lokacin da suka rike mukamai.

EFCC.
Adesola Amosu a hannun EFCC Hoto: @officialefcc
Asali: Facebook

Rahoton EFCC ya ce da aka gayyaci Akube domin ya fadi abin da ya sani, sai ya bada labarin yadda aka tura N2bn daga asusun NIMASA zuwa na sojojin sama.

Lauyan gwamnati ya bukaci wannan mutumi ya fadi inda kudin da aka turowa sojojin suka kare a karshe, sai ya ce an tura su ne zuwa wasu kamfanoni.

An ambaci wasu kamfanonin mai

A cewarsa kamfanonin su ne Delfina Oil & Gas Limited, McAllan Oil & Gas Limited Trapezites da BDC.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Masu Neman Shugabanci a Majalisar Wakilai da Dattawa

A bayanin da ya yi wa kotu a jiya, shaidan ya fadawa Alkali cewa kamfanin Divention Construction Limited yana cikin wadanda aka aikawa kudin.

Bayanan da aka fitar a shafin Hukumar binciken ya ce Air Marshall Adesola Amosu zai san matsayarsa nan gaba, sai 7 ga watan Yulin 2023 za a koma kotu.

Kananan hukumomi sun samu N2tr

Wani rahoto da muka fitar yana tattare da bayanan Biliyoyin da aka rabawa kananan hukumomin kasar nan 774 da ake da su a shekarar 2022 da ta wuce.

Kananan hukumomin Legas, Kano, Oyo, Ribas da Katsina sun samu N500bn. Jihohin Bayelsa, Gombe, Ebonyi, da Nasarawa sun samu mafi karancin kaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng