Kano da Jihohin da ke Gaba-Gaba Wajen Samun Kason Kudin Kananan Hukumomi a 2022

Kano da Jihohin da ke Gaba-Gaba Wajen Samun Kason Kudin Kananan Hukumomi a 2022

  • Kananan hukumomin da ke Najeriya sun tashi da abin da ya zarce Naira Tiriliyan 2 a shekarar bara
  • Alkaluma sun nuna jihohin Legas, Kano da Ribas su ne a kan gaba wajen samun kaso mai tsoka a kudin
  • Jihohin da suka tashi da kaso mara yawa su ne Bayelsa da Gombe masu karancin kananan hukumomi

Abuja - Rahoto ya zo cewa a shekarar 2022 da ta gabata, kananan hukumomi sun samu Naira Tiriliyan 2.02 daga asusun hadaka na FAAC.

Alkaluma sun tabbatar da cewa kananun hukumomin da ake da su a jihohin Legas, Kano, Oyo, Katsina da Ribas ne suka fi more wannan kudi.

Kananun hukumomin da ke jihohin nan biyar sun samu 24.83% na kudin kananun hukumomi 774, ma’ana su 144 sun tashi da kusan N500bn.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

A bangare dabam, an bar kananun hukumomin Bayelsa, Gombe, Ebonyi, Nasarawa da Ekiti a baya a wajen kason kudin da aka tara a asusun FAAC.

An bar kananan hukumomi 630 da N1.5tr

Rahoton ya ce kananun hukumomi takwas da ke jihar Bayelsa sun samu N24.03bn, sai N28.97 suka tafi zuwa ga kananun hukumomin Gombe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da aka akanana n hukumomin Ebonyi shi ne N31.73bn, Nasarawa da Ekiti masu kananan hukumomi 29 sun samu N31.96bn da N34.86bn.

Gwamnoni
Gwamnoni a Aso Rock Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Duka-duka, N37.69bn aka rabawa kananan hukumomin jihar Kwara 16, haka abin yake ga Zamfara da kananan hukumominta su ka samu N38.37bn.

FCT, Adamawa, Benuwai dsr

Yayin da jihar Abia ta samu N39.33bn, an raba N39.52 ga birnin tarayya Abuja mai kananan hukumomi shida rak, sai aka ba jihar Taraba N40.42bn.

Yobe ta samu N41.22bn, K/Ribas N41.69bn, Ondo N43.33bn, Enugu N43.42bn, Edo N43.54bn, Filato N44.33bn, Ogun N45.68bn sai N49.3bn a Adamawa.

Kara karanta wannan

Kashe tsoffin Naira: CBN ya yi maganar da kowa ya kamata ya sani kan hukuncin kotu

Delta ta samu N57.68bn, Imo kuwa N58.2bn sai N58.42bn a Osun, Neja ta tashi da N60.68bn kamar yadda Jigawa ta samu N65.37bn, Borno N66.31bn.

Anambra, Kebbi, Sokoto, Bauchi da Benuwai sun samu tsakanin N49bn zuwa N57bn a shekarar 2022, a karshe N67.69bn aka raba a Akwa Ibom, N80.39bn.

Dogayen layi a gidajen mai

An samu rahoto a baya cewa ana saida litar fetur a kan N400 a gidajen mai. ‘Yan bumburutu su na saida litarsu kuwa a tsakanin N450 zuwa N500.

Tun bayan zaben shugaban Najeriya da aka yi a karshen Fubrairu, motoci suka daina shiga jihohin Kudu domin dauko fetur a dalilin tsoron rikici ya barke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng