Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas

Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas

  • An samu aukuwar mummunan haɗarin jirgin ƙasa da wata mota ɗauke da fasinjoji a jihar Legas
  • Jirgin ƙasan yayi taho mu gama da wata mota wacce take ɗauke da fasinjoji yayin da take shirin tsallaka hanyar sa
  • An samu asarar rayuka yayin da mutane da dama suka samu raunika a harin da ya auku ranar Alhamis

Jihar Legas- Wani jirgin ƙasa ya haɗe da wata motar fasinjoji a yankin Shogunle na Oshodi a jihar Legas.

Lamarin ya auku da safiyar ranar Alhamis. Rahoton The Cable.

Shaidun gani da ido a inda lamarin ya auku sun bayyana cewa motar tana ƙoƙarin wucewa ta kan taragon jirgin ƙasan ne lokacin da wani jirgi mai tahowa yayi taho mu gama da ita.

Hadarin Jirgi
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas Hoto: The Punch
Asali: UGC

Jirgin ƙasan yayi tafiya mai nisa da motar inda tun daga Shogunle sai da ya kai ta yankin PWD a Ikeja.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mayaƙan Boko Haram Tsagin ISWAP Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Fasinjoji da dama sun samu raunika a haɗarin da ya auku.

Wasu daga cikin shaidun gani da idon sun bayyana cewa motar tana ɗauke ne da ma'aikatan gwamnatin jihar Legas.

Shaidun gani da idon sun tabbatar da cewa direban motar ya ƙi dakatawa ne a wajen tsayawa lokacin da aka tsayar da shi.

A cewar wani mai suna Babs wanda akayi haɗarin akan idon sa, yace lokacin da jami'an hukumar NRC suka dakatar da direban saboda jirgin dake tahowa sai ya ƙi ya tsaya.Ya ɗauka cewa zai iya wucewa kafin jirgin ya ƙara so.

Wani darekta a hukumar kiyaye haɗura ta jihar Legas, Adebayo Taofiq, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa. Rahoton Punch

“An samu raunika sosai a haɗarin domin motar cike take da ma'aikatin gwamnatin Legas waɗanda ke zuwa wajen aiki da safiyar nan."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta ba Tinubu damar yin kwafin takardun da INEC ta yi aiki dasu a zaben shugaban kasa

Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutum biyu sun rasu a haɗarin. Rahoton Daily Trust

“An ciro gawar wasu mata biyu ma'aikatan gwamnatin Legas, yayin da aka kwashe mutane da dama waɗanda suka samu raunika."

Ga wasu hotunan haɗarin a nan ƙasa:

Jirgi
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook
Jirgi
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook
Jirgi
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook
Jirgi
Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Legas Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook

Jiragen Yaƙin Sojin Sama Sun Halaka Wata Mata Mai Juna Biyu a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, jiragen yaƙin sojin sama sun halaka wata mata mai juna biyu a jihar Kaduna.

Sojin saman dai wasu ƴan bindiga suka hara, sai tsautsayi ya faɗa kan matar da wasu ƙananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng