Ana Daf Da Zabe, Yan Bindiga Sun Kona Gidan Dan Takarar PDP Da Na Mahaifinsa

Ana Daf Da Zabe, Yan Bindiga Sun Kona Gidan Dan Takarar PDP Da Na Mahaifinsa

  • Wasu yan bindiga da ba a tabbatar ko su wanene ba sun tafi gidan dan takarar majalisar jiha karkashin jam'iyyar PDP, Ifeanyi Ozoemena, sun cinna wa gidan wuta
  • Maharan sun kuma tafi gidan mahaifin Ozoemena nan ma sun banka wa gidan wuta suka jira sai da komai ya kone kurmus kafin suka tatattara kansu suka tafi
  • Ozoemena ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai nuna bakin ciki da bacin rai duk da cewa babu wanda ya rasa rai sakamakon harin, ya yi kira ga kwamishinan yan sandan jihar ya yi bincike kan lamarin

Jihar Imo - Wasu yan bindiga a ranar Talata sun tafi gidan dan takarar majalisar jiha, Ifeanyi Ozoemena, da ke kauyensu a karamar hukumar Okigwe, sun cinna wa gidan wuta.

Punch Metro ta tattaro cewa yan bindigan sun kuma kona wani gida mallakar mahaifin Ozoemena yayin harin da suka kai misalin karfe 2 na rana.

Kara karanta wannan

An Kama Wani Mai Gida Bayan Ya Kai Sunayen Masu Haya Gidansa Shaharariyar Matsafa Bayan Sun Samu Saɓani

Taswirar Jihar Imo
Yan bindiga sun kona gidan dan siyasa a Imo. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan siyasan ya tabbatar da harin

Dan siyasan yayin tabbatarwa The Punch harin ya ce, yan bindigan da suka ci karensu ba babbaka, sun janyo asarar dukiyan miliyoyin naira.

Ya ce:

"Sun kona gida na da na mahaifina a kauyen Umuokparaoha da ke garin Umulolo a karamar hukumar Okigwe na jihar Imo a ranar Talata.
"Sun kai harin ne misalin karfe 2 na rana, sun cinna wa gidajen wuta suka jira komai ya kone. Gidajen biyu da dukkan kayan da ke ciki sun lalace yayin harin. Ba wanda ya yi kokarin taka musu birki. Ina cikin wani hali. Abin bakin ciki ne."

Dan siyasan ya yi kira ga kwamishinan rundunar yan sanda ya dauki mataki.

Ya kara da cewa:

"Na gode wa Allah ba bu wanda ya rasa rai. Dattawan iyaye na ba su gida lokacin da suka kai harin."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Mutum 6 Sun Mutu, An Sace Wasu 50 Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Wata Jihar Arewa

Yan ta'adda sun kai mugunyar hari ofishin hukumar INEC a Imo, an sheke uku daga cikinsu

A wani rahoton a baya, kun ji cewa wasu yan bindiga sun kai mummunan hari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, da ke Owerri a jihar Imo.

Rahotanni daga jaridar The Punch sun nuna cewa maharan sun lalata wani sashi na ginin ofishin hukumar zaben sakamakon bam da suka dasa ya tashi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Imo. Mike Abattam ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce an kashe uku cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164