Ba Mu Umurci Bankuna Su Ci Gaba da Ba da Tsofaffin Takardun Naira Ba, CBN Ya Magantu

Ba Mu Umurci Bankuna Su Ci Gaba da Ba da Tsofaffin Takardun Naira Ba, CBN Ya Magantu

  • A halin da ake ciki, bankunan Najeriya sun fara ba da tsoffin kudi ga kwastomomi bayan hukuncin kotun koli a makon jiya
  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce bai ba da wani umarni a hukumance ba kan bankuna su ci gaba da ba tsofaffin kudin ba duk da hukuncin kotun
  • ‘Yan kasuwa da kwastomomi na cikin rudani kan halin da ake ciki na karancin Najeriya da kuma hukuncin kotu na kwanan nan

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Talata ya bayyana cewa, bai ba da wani umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin kotu koli na ranar Juma’ar da ta gabata na ci gaba da kashewa da ba da tsoffin Naira ba.

Idan banku manta ba, kotun kolin Najeriya ya yanke hukunci ga karar gwamnoni, inda yace za a ci gaba da ta’ammuli da tsoffin N200, N500 da N1000 har zuwa karshen watan Disamban bana.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Bullo Yayin da Bankuna Suka Fara Zuba Tsoffin N500 da N1000 a ATM

Rahotanni sun bayyana yadda aka samu rudani tsakanin ‘yan kasuwa da bankunan kasar kan rashin cewa komai da CBN ya yi game da hukuncin kotun.

CBN ya warware batu, ya ce bai umarci bankuna su ci gaba da ba tsoffin Naira ba
Sauya Naira a Najeriya ya haifar da cece-kuce mai daukar hankali | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

CBN ya magantu kan matsayarsa

Mai magana da yawun CBN, Isa Abdulmumini ya zanta da jaridar DailyTrust, inda ya ce babban bankin bai ba da wata sanarwa a hukumance kan ci gaba da ba da tsoffin kudaden ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, duk da haka wani babban ma’aikacin bankin ya shaidawa jaridar a wata tattaunawa cewa:

“Tsoffi da sabbin kudi duk sun halasta a kashe, kuma bankuna a yanzu haka suna ba kwastomomi. Kada ‘yan Najeriya su ki karbar kudi, tsoho ko sabo.”

Bankuna har sun fara ba da tsoffin kudi, wasu kuma shuru

Sai dai, kamar bankuna sun yi riga-malam masallaci, domin bincike a wasu bankunan kasar nan da aka yi ya nuna, tuni sun fara raba tsoffin kudaden ga kwastomominsu; musamman ‘yan N500 da N1000.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: CBN Ya Amince a Ci Gaba da Amfani da Tsoffin Naira, Sabbin Bayanai Sun Fito

A Legas, wasu daga bankunan GT, Zenith da WEMA tuni suka fara sanya kudaden a injunan ciran kudi na ATM da kuma ba da kudin a kan kanta.

A bangaren wasu bankunan kuma kamar First Bank, Poliris da Unity, ba a fara ba da kudaden ba ga kwastomomi, kuma babu wani karin bayani.

‘Yan kasuwa; wasu na karba, wasu sun yi shuru

Hakazalika, ‘yan kasuwa da yawa sun ki karbar wadannan kudade duk da kuwa da umarnin kotun don gudun asara idan CBN ya fadi sabanin abin da kotu yace.

Babban kantin siyayya na San-Hussein a tsakiyar jihar Gombe ba ya karbar tsoffin kudaden, inda ma’aikatan kantin suka ce umarni ne daga sama.

A bangare guda, wani mai shagon kayan masarufi a unguwar Pantami, Sani Muhammad ya ci gaba da karbar kudaden har zuwa safiyar yau Laraba 8 ga watan Maris.

Ga abin da yake cewa:

“Eh, tunda aka fada a rediyo cewa za a ci gaba da karba nima na fara, akwai uban gidana, ba zai rasa hanyar shigar da kudaden ba ko da kuwa a CBN kuma na yi magana dashi.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Baya Ga Dogon Layi a Banki, Kwastomomi Sai Sun Ba Da Cin Hanci Kafin Su Iya Shiga Banki

“Mutane suna da tsoffin kudin nan, musamman masu shigowa daga kauyuka, karbar zai taimake su wajen shigar da kudaden.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.