Rikicin Naira: Ana Ci Gaba Da Layi Don Samun Tsabar Kudi, Kwastamomi Na Baiwa Jami’an Banki Cin Hanci

Rikicin Naira: Ana Ci Gaba Da Layi Don Samun Tsabar Kudi, Kwastamomi Na Baiwa Jami’an Banki Cin Hanci

  • Har yanzu ana fuskantar cunkoso yayin gudanar da hada-hadar kudi a bankuna a fadin kasar
  • Saboda matsalar karancin tsabar kudi, kwastamomi sun koma ba ma'aikatan banki cin hanci domin samun hanyar shiga cikin sauki
  • Mutane sun koka kan yadda suke shafe awanni a kan layi ba tare da kudi ya kai kansu ba

Ana ci gaba da jan dogon layi a bankuna a fadin kasar yayin da kwastamomi ke fafutukar cire tsabar kudi, duk da hukuncin kotun koli da ya ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudi har zuwa 31 ga watan Disamba, Daily Trust ta rahoto.

A ranar Juma'a ne wani kwamitin mutum bakwai na kotun koli ya yanke hukunci cewa tsoffin N200, N500 da N1000 na da inganci har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

IWD2023: Mata 13 da Za Suyi Kafada da Kafada da Maza a Majalisa Bayan Nasara a Takara

Jama'a tsaye a bakin banki
Rikicin Naira: Ana Ci Gaba Da Layi Don Samun Tsabar Kudi, Kwastamomi Na Baiwa Jami’an Banki Cin Hanci Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto cewa har yanzu ana fama da dogayen layuka a yawancin bankunan Abuja, Kano da Lagas.

Ma'aikatan banki na karbar cin hanci daga kwastamomi

An kuma tattaro cewa wasu kwastamomi da ke neman tsabar kudi ido rufe suna bayar da cin hanci ga ma'aikata da masu tsaron bankuna don samun tsaba a hannu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani kwastama a Kano, Shuaibu Muhammad Haruna, wanda ya ce ya isa bankin tun da misalin karfe 6:00 na safe, bai samu shiga bankin ba har zuwa 2:15 na rana.

Ya ce irin haka ya faru da shi a makon jiya, amma da ya zo kansa, sai aka ce kudin ya kare.

"Duk dadewar da za ka yi a kan layi, ba za su baka abun da ya fi N10,000 ba wasu ma N5000 suke bayarwa," in ji shi."

Kara karanta wannan

Shirin zabe: Ana shirin zabe, gwamnonin APC sun shiga zaman kus-kus da shugaban jam'iyya

Wani kwastaman, Yusufu Usman, ya ce:

"Sai da na yi tiransfa din N11,000 zuwa asusun wani mai tsaron banki don ya tayani cire N10,000. Wannan ne abun da ke faruwa kimanin tsawon watanni biyu yanzu."

Wata mata da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce ta samu kudi daga banki ne cikin sauki saboda ta san daya daga cikin ma'aikatan.

"Na zo nan da rana kuma ban dauki awa biyu ba. Na san daya daga cikin ma'aikatan bakin da na kira shi, na samu shiga bankin ba tare da na bi layin ba."

Halin da kwastamomi suka tsinci kansu a Abuja

A Abuja, yawancin bankuna sun cika da kwastamomi. An kuma tattaro cewa yawancinsu sun hallara ne don yin korafi a kan hada-hadar kudi da ya kakare.

Kwastamomi da dama da suka isa bankunansu don yin hada-hadar kudi sun nuna rashin jin dadi kan yadda aka hana su shiga.

Da take bayyana halin da ta tsinci kanta a daya daga cikin bankunan, Abike Oladapo, ta ce ta isa banki da karfe 7:00 na safe don yin korafi game da wani hada-hadar kudi da ya kakare.

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

Sai dai ga mamakinta, ta ga mutane sun rigada sun yi layi a bankin suna jira a bude domin fara harkokin ranar.

Legit.ng ta tuntubi wasu daga cikin mazauna garin Minna, babban birnin jihar Neja inda suka ce suma haka abun take a bangarensu.

Hajiya Fati Abubakar ta ce:

“Wallahi tun kusan sati biyu kenan ina neman kudi ban samu ba, ko yara haka nake tura su makaranta yanzu da abun da ya sawaka ko kudin kashewa a makaranta bana basu nace sai dai su yi hakuri. Allah dai ya kawo mana karshen wannan abu.

Mallam Hussaini kuwa ya ce haka ya gama bata lokaci a banki amma bai samu abun da ya je nema ba.

Ya ce:

“Da asubahi bayan na bar masallaci na bi layin banki sai dai har zuwa karfe 10:00am ban samu kudi ba a karshe hakura na yi naje wani POS da ke nan hanyar Mandela na samu ya bani N2000 bayan na biya N100.”

Kara karanta wannan

Shin Kwankwaso Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Tinubu Murna, NNPP Ta Yi Karin Haske

Bankuna sun ci gaba da bayar da tsoffin kudi a Abuja da Kano

A baya mun ji cewa wasu bankuna a jihohin Kano, Ibadan, Abuja da Lagas sun ci gaba da bayar da tsoffin kudi na N500 da N1000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel