Gwamnan Jihar Edo Ya Roki Mata Su Taimake Shi Kada Ya Fadi a Zaben Bana
- Gwamnan jihar Edo ya nemi tallafin mata a zaben 'yan majalisu da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa
- Gwamnan ya ce APC na shirin kawo tsaiko ga zaben 11 ga watan Maris da za a yi jihar ta Edo
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da shirin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi a Najeriya
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bukaci mata a jiharsa da su taimake shi su kubutar dashi daga tsigewa ta hanyar zaben jam’iyyar PDP a zaben 11 ga watan Maris mai zuwa na ‘yan majalisun dokokin jiha.
Obaseki ya bayyana hakan ne a karshen mako yayin da yake ganawa da mata daga gundumomi 12 na karamar hukumar Oredo tare da neman kuri’unsu ga 'yan takarar PDP.
Gwamnan ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Osaigbovo Oyoha ne a taron, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wakilin gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin Obaseki za ta duba tare da habaka jin dadin mata da rayuwarsu a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
APC na shirin kawo tsaiko ga zaben gwamna
A cewarsa, jam’iyyar APC na shirin yadda za ta kawo tsaiko ga dukkan ababen alheri da gwamnan yake yi a jihar Edo, inda ya yi kira ga jama’a da su guji jam’iyyar ta APC da ‘yan takararta, Daily Sun ta tattaro.
Ya bayyana cewa:
“Zaban PDP a majalisar dokoki zai taimakawa ci gaban da muke aiki akai. Zaben nan na gwamna Godwin Obaseki ne don kawai ya ci gaba habaka ci gaban jihar da kuma habakawa da inganta rayuwar al’ummar jihar.
“Jam’iyyar APC na nan na ta shirin murdiya a zaben 11 ga watan Maris don ganin sun tsige gwamnan tare da tsayar da ayyukan ci gaba da za su amfani al’ummar jihar Edo.
“Muna rokon jama’a da su zabi PDP tare da tsayar da makiya al’ummar jihar Edo daga dakatar da ci gaban da aka dauko yiwa jama’a. Dukkan kuri’unmu dole su zama daya. Dole su zabi PDP dodar.”
Ku zabi PDP daga sama har kasa
A nasa bangaren, daraktan kamfen na PDP a jihar Edo, Cif Osaro Idah ya roki mata a jihar da su yi gangamin tallata dukkan ‘yan takarar PDP a zaben mako mai zuwa.
Bugu da kari, shugabar matan karamar hukumar ta Oredo, Meg Aigbohae ta ba da tabbacin cewa, mata za su kada kuri’unsu ne ga jam’iyyar PDP a zaben ‘yan majalisun dokoki.
Bayan kammala zaben shugaban kasa lafiya, gwamnonin PDP sun maka INEC a kotu, amma daga baya suka janye karar.
Asali: Legit.ng