Jama’a Sun Tsere Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Hedkwatar Karamar Hukuma a Zamfara, Sun Kashe DPO Da Wasu 2
- Yan bindiga sun sake kai hari Zamfara, inda suka jefa jama'a cikin halin tashin hankali yayin da suka bazama neman tudun tsira
- Wani DPO da wasu mutum biyu sun hadu da ajalinsu l0okacin da yan bindigar suka kai farmaki hedkwatar karamar hukumar Maru
- Wata majiya ta bayyana cewa an yi garkuwa da wasu mazauna da ba a san adadinsu ba kuma an bazama binciken inda suke
Zamfara - Wani DPO da wasu mutane biyu sun rasa rayukansu lokacin da wasu yan bindiga suka farmaki hedkwatar karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a daren ranar Asabar, 4 ga watan Maris, rahoton Punch.
Channels TV ta rahoto cewa mazauna yankin sun tsere don neman mafaka yayin da yan bindigar suka farmaki Maru sannan suka dungi harbi kan mai uwa da wahabi.
Bayan samun bayani kan harin, DPO na karamar hukumar, Kazeem Raheem, ya tattara jami'ansa da wasu yan sa-kai don dakile harin.
Abun bakin ciki, DPOn, wani sajan mai suna Rabiu Bagibiri da wani dan sa-kai mai suna Shehu Chuka, sun rasa ransu yayin da suke dakile harin yan bindigar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yanzu haka, hukumomin yan sanda a Maru suna yawon gani da ido, kamar yadda kakakin yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya bayyana.
Yan bindiga sun sace mazauna Maru
Wata majiya daga hedkwatar karamar hukumar ta fada ma Channels TV cewa yan bindigar sun sace wasu adadi na mazauna yankin.
Wata majiya wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa:
"Sun sace mutane, amma ba a san adadinsu ba zuwa yanzu, har yanzu suna neman mutanen da suka gudu don tsira da rayuwars."
Yan Boko Haram sun koma yin shigar mata yayin kai hari, Sanata Ndume
A wani labarin, Sanatan Borno, Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram sun koma yin shigar mata yayin kai hari kan al'umma a jihar Borno.
Ndume ya bayyana cewa a harin baya-bayan nan da Boko Haram suka kai garinsa, sun kasance sanye da tufafin mata wajen kai harin da ya yi sanadiyar rasa ran mutum daya tare da jikkata wasu da dama.
Asali: Legit.ng