Sojoji Sun Halaka Dan Ta'adda A Kaduna, Sun Kubutar Mutum 14 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Halaka Dan Ta'adda A Kaduna, Sun Kubutar Mutum 14 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani dan bindiga sannan sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su
  • Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da hakan yana mai cewa sojojin sun kuma kwato babur tare da lalata sansanin yan bindigan
  • Aruwan ya kuma ce gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi farin cikin samun labarin, ya kuma yaba wa sojojin karkashin jagorancin Manjo Janar T.A. Lagbaja

Jihar Kaduna - Dakarun sojojin Operation Whirl Punch, da Dakaru na musamman na Bataliya ta 167 sun kashe wani dan ta'adda sannan sun ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su, rahoton Daily Trust.

Dakarun sojojin wadanda suka fara sintiri mai tsawo tare da yakar masu laifi a Tukurua da ke karamar hukumar Chikun a jihar sun fafata da yan bindiga sun kuma kore su daga sansaninsu bayan fafatawa mai zafi a yankin.

Dakarun Sojoji
Dakarun sojojin Najeriya. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Samuel Aruwan, kwamishinan na harkokin cikin gida da tsaro, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce:

"Sojojin a yayin aiki sun ceto mutane 14 daga hannun masu garkuwa, wadanda suka hada da mata biyar da maza tara. An kai wadanda abin ya shafa wani wuri mai tsaro don tantancewa kafin a sake su su tafi wurin iyalansu."

A cewarsa, yayin arangamar, sojojin sun lalata sansanin yan ta'adda da dama kuma sun kwato babura biyu, The Punch ta rahoto.

Gwamna El-Rufai ya jinjina wa sojoji a Kaduna

Ya ce Gwamna Malam Nasir El-Rufai wanda ya nuna farin cikinsa ga rahoton, ya yaba wa shugabancin Manjo Janar T.A. Lagbaja, GOC na One Division kuma kwamandan Whirl Punch.

Gwamnan ya kara yabawa kwazon sojojin, domin an kubutar da daukacin ‘yan kasar da aka yi garkuwa da su a raye ba tare da wani rauni ba.

A wani rahoton hukumar ICPC ta cafke wani Hassan Ahmed da takardun naira da suka hada da sabbi da tsaffi a yayin da ake fama da karancin kudi.

Sojojin Najeriya na 33 Artillery Birgade da ke sintiri a Alkaleri Bauchi ne suka kama mutumin da kudin cikin jaka ta 'Ghana must go' sannan suka kai shi wurin ICPC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164