Kotun Daukaka Kara Ta Ba Atiku da Obi Damar Bincika Takardun Zaben Shugaban Kasa Na Bana
- ‘Yan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin jam’iyyar Labour da PDP sun samu damar duba takardun zaben shugaban kasa
- Atiku Abubakar da Peter Obi sun ce basu amince da sakamakon zaben shugaban kasan da aka yi ba a Najeriya ranar Asabar
- Jam’iyyar APC ta ce babu damuwa, a hadu a kotu tsakanin Tinubu da Peter Obi da kuma Atiku Abubakar
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara ya ba Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour damar duba takardun aikin zabe na INEC don gano yadda zaben 25 ga watan Faburairu na shugaban kasa ya wakana.
Har ila yau, kotun ya ba da irin wannan dama ga dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar don tabbatar ba a cuce su a zaben ba.
Wannan na zuwa ne a cikin wani zama da kotun ya yi karkashin jagorancin mai shair’a Joseph Ikyegh a ranar Juma’a 3 ga watan Maris, TheCable ta ruwaito.
Kotun ya saurari kararraki guda biyu da ‘yan takarar biyu suka shigar na neman hujjar kalubalantar sakamako da ingancin zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda zaben shugaban kasa a Najeriya ya kasance
Idan baku manta ba, an yi zabe tare da ayyana Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 8,794,726.
Atiku Abubakar ya zo na biyu, inda ya tashi da kuri’i 6,984,520, sai kuma Peter Obi a na uku tare da kuri’u 6,101,533.
Atiku da Obi dai sun ce sam ba za su amince da sakamakon ba, don haka suka garzaya kotu don bayyana kokensu a can, rahoton Punch.
Abin da suka nema a kotu a yanzu
A gaban kotun, dukkan ‘yan takarar biyu sun nemi kotun da ya umarci hukumar zabe ta INEC ta ba su damar duba takardun da aka yi amfani dasu a zaben shugaban kasa na bana.
Sun bayyana cewa, wannan ne zai ba su damar tabbatar da aniyarsu ta kalubalantar nasarar Tinubu a gaban kotun gaba.
Wadanda aka shigar kara a wannan batu dai ba kowa bane face hukumar zabe ta INEC, Bola Ahmad Tinubu da kuma jam’iyyar APC mai mulkin kasar.
A bangare guda, jam’iyyar APC ta ce a shirye take don karbar kalubalen da ‘yan takarar biyu suka shigar a kotu.
Asali: Legit.ng