Daruruwan ’Yan Boko Haram Sun Hakura da Ta’addanci, Sun Ajiye Makamai a Borno

Daruruwan ’Yan Boko Haram Sun Hakura da Ta’addanci, Sun Ajiye Makamai a Borno

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu ‘yan ta’addan Boko Haram sun ajiye makamai tare da mika wuya ga sojin Najeriya
  • Akalla ‘yan ta’adda 199 ne suka ajiye makamai, inda da mika wuya tare da iyalansu a Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Ana ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’adda a bangarori da yawa na kasar nan, musamman Arewa maso Gabashin kasar

Jihar Borno - Daruruwan ‘yan Boko Haram ne suka mika wuya tare da ajiye makamai a cikin kwanaki hudu bayan da suka samu sabani da kazamin fada a tsakaninsu.

Hakazalika, ragargazar da rundunar sojin sama da na kasa na Najeriya suka yi sa daruruwan ‘yan ta’addan sun tsere daga sansaninsu da ke Gaizuwa a Bama da ke jihar Borno.

'Yan ta'adda sun mika wuya ga soji a Borno
Taswirar jihar Borno mai fama da barnar Boko Haram | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

‘Yan ta’addan da aka kama da wuraren da aka kama su

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

A cewar rahoto, ‘yan ta’addan 119 ne tare da iyalansu suka mika wuya tare da ajiye makamai ga jami’an rundunar Operation Hadin Kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu kuwa sun mika wuya a Konduga, yayin wasu suka tsere ta yankin Dikwa da ke bullewa suka tafkin Chadi, kafar Labarai ta Zagazola Makama ta tattaro.

Hakazalika, da yawan ‘yan ta’addan sun mika wuya tare da ajiye makamai da kayan fashewa ga jami’an tsaro a kusa Gueskerou a Diffa da ke jamhuriyar Nijar.

Duba da yadda abubuwa ke tafiya, ‘yan ta’addan Boko Haram sun amsa ‘yan ta’addan ISWAP sun fi karfin su a yankunan da kungiyoyi biyun ke aikata ta’addancinsu.

Ana ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’addan a bangarori daban-daban na Najeriya, kamar yadda rahotanni da alkaluma ke nunawa.

‘Yan Boko Haram sun kai hari kan mazauna Goza a jihar Borno

Kara karanta wannan

Daga sintirin sa ido: 'Yan daba sun yi kaca-kaca da tawagar EFCC a filin zabe a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka farmaki al’ummar Goza a jihar Borno ba a ranar Asabar, ranar da aka yi zaben shugaban kasa a Najeriya.

Sarkin Goza, Mohammed Shehu Timta ya tabbatarwa majiya wannan lamari, inda ya ce an farmaki mutanen garinsa ne a lokacin da suke kokarin kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar.

Ya ce:

"Kungiyar Boko Haram ta kawo mana hari har cikin kwaryar gari, suka bude wuta kan mai uwa da wabi, mutane 5 suka ji raunuka kuma tuni aka garzaya da su Asibiti a Maiduguri domin kula da lafiyarsu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.