Dalilin da Yasa Tinubu Ya Fadi a Legas, Obi Ya Lashe Zabe, Bayanin Dele Momodu
- Jigon jam’iyyar PDP, Dele Momodu ya bayyana mahangarsa ga yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya lashe a Legas
- A cewarsa, Obi ya samu kuri’un Legas ne saboda yadda Inyamurai suka mamaye birnin Legas suke rayuwarsu a ciki
- Sai dai, ya kuma dasa alamar tambayar yadda dan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi nasara a zaben bana na 2023
Jigon jam’iyyar PDP, Dele Momodu ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya lashe kuri’un jihar Legas.
Momodu ya bayyana cewa, Obi ya ci kuri’un Legas ne saboda da yawan mazauna jihar Inyamurai ne da suka kama wuri suka zauna a cikin jihar.
Da yake zantawa da gidan talabajin na Channels, Momodu ya ce, mamayar Inyamurai a ko ina a Legas ne ya sa jam’iyyar APC da PDP basu samu kuri’un da suka kai na Peter Obi ba.
Dalilin nasarar Obi a Legas
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake bayani ga gidan talabijin din, Momodu ya ce:
“Abin da ya faru a zaben ranar Asabar, babban abin da ya faru lamari ne na kabilanci: jam’iyyar Labour ta samu damar lallasa APC ne saboda yadda Inyamurai suka mamaye jihar Legas. Suna nan a ko ina.”
Momodu, wanda shine jagora a gangamin kamfen PDP, ya ce Obi da Atiku sun yi nasarar lashe yankunansu, amma kuma abin tambaya ne yadda Tinubu ya gasa nasara a yankinsa.
Hakazalika, ya ce duk da Tinubu ya fadi a jiharsa, abin mamaki ne yadda aka ba shi shaidar nasara a zaben na bana.
A cewarsa:
“Lalataccen tsari ba ya taba haihuwar tsari mai kyau. Ba a bi ka’idar dokar zabe ba. Don haka, duk wanda ya ci zaben ranar Asabar, bai iya yace an yi gaskiya ba. Wancan tsarin dai shi ya haifar da cece-kucen da ake dashi a yanzu.”
Idan baku manta ba, Obi na ba Tinubu kuri'u kusan 10000 a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Faburairun 2023, lamarin da ya jawo cece-kuce a siyasar kasar.
Asali: Legit.ng