Bola Tinubu Zai Yi Kaura Zuwa Defence House Na Gwamnati da Ke Abuja
- Bayan lashe zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kaura gadan-gadan zuwa cikin wani gida a Abuja
- An ruwaito cewa, Tinubu zai koma rayuwa a cikin Defence House da ke Maitama a FCT kafin zarcewa Villa
- Har yanzu ana ci gaba da taya Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa, El-Rufai ma ba a bar shi a baya ba
FCT, Abuja - Zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kaura zuwa daya daga cikin gidajen gwamnatin Najeriya, Defence House da ke Abuja.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da aka sanar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Asabar 25 ga watan Faburairu.
Idan banku manta ba, an yi zabe a Najeriya kuma Tinubu ne ya samu kuri’u sama da miliyan takwas, inda ya lashe zaben da ke da ‘yan takara 18.
Biyo bayan sanar da nasararsa, jam’iyyun PDP da Labour sun bayyana rashin amincewa, inda aka ce sun garzaya kotu domin tabbatar da an sake yin zabe a kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu zai kaura zuwa Defence House a Maitama
A bangare guda, tawagar gangamin kamfen a APC ta fitar da wata sanarwa da cewa, Tinubu zai koma karkashin kulawar gwamnati a matsayinsa na sabon zababben shugaban kasa.
A cewar APC, wannan ne somin tabi na kama aikin shugabancin kasa da Tinubu zai yi a matakin farko.
Hakazalika, an ce zai shafe watanni ne a Defence House kafin daga bisani a rantsar dashi ya shige fadar shugaban kasa don kama aikin hidima ga Najeriya gadan-gadan.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Zabebben shugaban kasa zai kaura zuwa Defence House a cikin Maitama, FCT, inda zai zauna na tsawon watanni, inda naga nan zai zarce fadar shugaban kasa ta Villa.”
Har yanzu ana ci gaba da aiko sakwannin murna ga Bola Tinubu tun bayan da ya lashe zaben shugaban kasa.
Gwamna El-Rufai ya taya Tinubu murna
A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnan jihar Kaduna ya fito ya taya Bola Tinubu murnar samun nasarar lashe zaben shugaban kasa na bana.
El-Rufai ya bayyana cewa, yana da yakinin Tinubu zai yiwa ‘yan kasa abin da ake tsammani na alheri tare da ciyar da kasar gaba.
Hakazalika, ya ce Tinubu mutum ne mai hangen nesa, kuma tabbas zai kawo sauyi mai nagarta na kasa.
Asali: Legit.ng