Zaben 2023: Amurka Ta Taya Tinubu Murna, Ta Ba Wa Sauran Yan Takara Shawara
- Kasashen duniya sun fara taya zababben shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu murnar cin zabe
- Amurka ta taya Tinubu murna sannan ta yi kira ga yan Najeriya su zauna lafiya, masu korafi kuma su tafi kotu
- Shima faraiministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya taya Tinubu murnar nasarar lashe zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Janairu
Kasar Amurka, a ranar Laraba ta taya Najeriya murna kan zaben Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress mai mulki a kasar matsayin shugaban kasa kuma ta yi kira a kwantar da hankali kan zargin magudi da matsalar na'ura, rahoton The Punch.
A ranar Talata ne aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ne a ranar 25 ga watan Fabrairu a kasar bakar fata wacce ta ci shahara a duniya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasar waje na Amurka Ned Price ya ce:
"Amurka na taya mutanen Najeriya, zababben shugaban kasa Tinubu da dukkan shugabannin siyasa."
Ya kara da cewa:
"Wannan zaben da aka fafata kansa na wakiltar sabuwar siyasa da dimokradiyya a Najeriya."
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, Tinubu, dan takarar na jam'iyyar APC da ke mulki a kasa, ya lashe zaben da kuri'u miliyan 8.8.
Sai wanda ya zo na biyu a zaben, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu miliyan 6.9 sannan Peter Obi na jam'iyyar Labour ya samu kuri'u miliyan 6.1.
Price ya shawarci wadanda ba su gamsu da zaben ba su tafi kotu
Price ya lura cewa akwai wasu yan Najeriya da ke nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben, duba da cewa a kalla daya cikin yan takarar an hamayya ya yi alkawarin zuwa kotu don kallubalantar sakamakon.
Ya ce:
"Mun fahimci cewa yan Najeriya da dama da wasu jam'iyyu sun nuna rashin gamsuwa da yadda aka yi zaben.
"Tabbas yan Najeriya na da damar nuna damuwarsu kuma su yi fatan ganin hukumar zabe ta gamsar da su," Price ya ce, yayin da ya ke kira ga shugabannin siyasa su bi hanyar da doka ta dace don gabatar da korafinsu wato "kotu".
Jami'an Najeriya sun yi fatan sabon nau'rar zaben zai kara taftace zaben kasar, amma matsaloli, jinkiri wurin fitar da sakamakon zabe ya asassa zargin magudin.
Price ya yi kira ga dukkan bangarori su guji rikici ko furta maganganu da za su iya tada hankula.
Rishi Sunak, Farai Ministan Birtaniya ya taya Tinubu murnar cin zabe
Shima Faraiministan Birtaniya, Rishi Sunak ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben, cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng