El-Rufai Ya Taya Bola Tinubu Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023 da Aka Yi
- Gwamnan jihar Kaduna ya taya Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa a zaben bana
- El-Rufai ya ce yana da yakinin Tinubu zai kawo ci gaba mai dorewa a Najeriya tunda aka bashi dama a yanzu
- Ana ci gaba da aika sakwanni murna ga Bola Tinubu tun bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe
Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya siffanta nasarar Bola Ahmad Tinubu da abin da ya cancanta kuma abin da zai kawo sauyi a Najeriya, rahoton TheCable.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na taya murna bayan da aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Idan baku manta ba, da sanyin safiyar ranar Laraba ne shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da cewa, Tinubu ya yi nasara a zaben 25 ga watan Faburairu da kuri’u 8,794,726.
A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon murnar El-Rufai ga Tinubu
A sakonsa na taya murna, El-Rufai ya ce yana da kwarin gwiwar Tinubu zai mulki Najeriya kuma ya ciyar da ita gaba, rahoton Vanguard.
Gwamnan na Kaduna ya kuma bayyana cewa, nasarar ta zo wa Bola Tinubu ne a lokacin da ya dace.
A cewarsa:
“Ya rataya a wuyan APC ta biya bashin da ke kanta ta hanyar yin mulki nagartacce da zai kawo ci gaba ga ‘yan Najeriya.
“Bana shakkar cewa Asiwaju Bola Tinubu ya fahimci nauyin wannan nasarar kuma zai mulki Najeriya ta ci gaba tare sabunta fatan ‘yan kasa.
“Ya san yana da goyon bayanmu wajen tattara ‘yan Najeriya da hada kan kasar ta hanyar bai daya don ci gaba da zaman lafiya.”
Mai Mala Buni ya taya Tinubu murnar gaje Buhari
A wani labarin, kunji yadda gwamnan jihar Yobe ya aiko da sakon taya murna ga Bola Ahmad Tinubu bayan sanar da ya kashe zaben bana.
Gwamnan ya ce ‘yan Najeriya sun yi abin da ya dace, kuma zai ciyar da kasar gaba ta hanyoyi da yawa.
Hakazalika, gwamnan ya ce yana fatan a samu sauyin da ake tsammani daga shugaban da aka zaba a bana.
Asali: Legit.ng