“Oluremi Ba Za Ta Koma Majalisa Ba”: Zababben Shugaban Kasa, Tinubu Ya Fadawa Sanatoci
- Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce ba zai bari matarsa ta koma majalisar dattawa ba duk kuwa da cewa ta lashe zaben sanata
- Wannan na zuwa ne a jawabinsa bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya
- Idan baku manta ba, an yi zaben shugaban kasa a Najeriya a ranar 25 ga watan Faburairu, Tinubu ne ya lashe zaben a cewar INEC
FCT, Abuja - Zababben shugaban kasa a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce, matarsa, Sanata Oluremi Tinubu ba za ta koma majalisar dattawa.
Ya bayyana hakan ne bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka yi a karshen makon jiya.
Ya shaidawa abokan aikinta a majalisa cewa, kada ma su yi tsammanin sake ganinta a cikin zauren majalisar a nan kusa, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.
Tinubu dai ya yi magana ne a ranar 1 ga watan Maris a babban birnin tarayya Abuja a jawabinsa na nuna godiya ga ‘yan Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Uwar gidan shugaban kasa, kuma cikakkiyar mai daki na za ta zama, cewar Tinubu
A cewarsa, matar tasa za ta yi aikinta ne a matsayinta matar gida, kuma uwar gidan shugaban kasan Najeriya.
A cewar Tinubu:
“Gare ki matata abar kaunata, Oluremi Tinubu, ku sanataoci, kada ku yi tsammanin za ta dawo, za ta kasance matat gida na kuma uwar gidan shugaban kasa.
“Rancen ya isa haka, idan baki gaji dani ba a yanzu, ba zan gaji dake ba. Ina cikin farin ciki.”
An yi zabe a Najeriya, kuma Bola Tinubu ne ya yi nasarar lashe zaben, kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta sanar a ranar Laraba 1 ga watan Maris.
Ku yi koyi da Jonathan, Tinubu ga sauran 'yan takarar shugaban kasa
A bangare guda, Tinubu ya shawarci abokan hamayyarsa da su yi hakuri idan suka fadi zabe su amince da abin da sakamako ya zo dashi.
Tinubu ya ce, ya kamata Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP su yi koyi da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.
A baya, 'yan takarar shugaban kasa a LP da PDP na duba yiwuwar neman a dakatar da tattara sakamakon zabe tare da sake yin zaben a wasu wurare.
Asali: Legit.ng