2023: Jam'iyyar NNPP Ta Kwankwaso Ta Fada Wa INEC Ta Soke Zabe, A Sake Sabo

2023: Jam'iyyar NNPP Ta Kwankwaso Ta Fada Wa INEC Ta Soke Zabe, A Sake Sabo

  • Rufai Alkali, shugaban NNPP na kasa ya yi kira ga hukumar INEC ta dakatar ta tattara sakamakon zabe da ake yi a Abuja
  • Alkali ya yi korafin cewa INEC ta hada kai da jam'iyyar APC mai mulki don tafka magudi a matakai da dama na zaben
  • Bisa dalilan zargin rashin adalci a harkar zaben ne jam'iyyar ta NNPP ta ce INEC ta zabi wani sabon ranar da za a sake zabe

FCT, Abuja - Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta yi kira da a soke babban zaben da aka yi a kasar nan take.

Rufai Alkali, shugaban jam'iyyar ta NNPP na kasa, a halin yanzu yana jawabi wurin taron manema labarai, The Cable ta rahoto.

Rufai Alkali
Shugaban NNPP na kasa Rufai Alkali da wasu jami'an jam'iyyar. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Sheikh Bala Lau Ya Gargadi Yan Siyasa Kan Furta Maganganu Da Ka Iya Tada Rikici

Ya ce yayin zaben, an samu matsaloli da dama kamar tauye hakkin masu kada kuri'a, tsoratarwa da kuma siyan kuri'u.

Alkali ya kuma yi kira ga hukumar zaben mai zaman kanta na kasa, INEC, ta sanar da sabon ranar da za a sake zabukan.

Ya ce:

"Muna damuwa bisa abin da ya faru ranar zabe, hukumar zabe ta mayar da kasar mu baya kafin 2015 inda ake duk abin da aka ga dama, inda ake tauye hakkin masu zabe da gangan, inda sace akwatin zabe da magudi ya yawaita, inda rikici da kiyan kuri'a ne ke nuna wanda zai ci zabe, inda jami'an tsaro ke goyon bayan jam'iyya mai mulki wurin yin magudi, kuma inda wadanda ba su yi takara ba ke cin zabe.
"Misali, a Kano, Ibrahim Shekarau, wanda ya fita daga NNPP a hukumance, ya janye daga takara, ya yi rajista da PDP, ya sanar da jam'iyya da INEC, amma yanzu INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe a karkashin NNPP. Abin takaici, wannan shine zamanin da hukumar zabe ta mayar da kasar mu."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Duk Wanda Bai Gamsu Da Sakamako Ba Ya Tafi Kotu", Martanin INEC Ga PDP Da LP

Shugaban na NNPP ya cigaba da zayyana kallubale da dama da suka fuskanta daga INEC tun farkon fara zabe har zuwa zaben cikin gida a matakin jiha da kasa.

Daga cikin jawabin ya ce:

"Wanda ya fi bada kunya shine yadda INEC ta ki amfani da tambarin jam'iyyar na ainihi a takardar kada kuri'a. Rashin amfani da tambarin mu na ainihi takardar kada kuri'a a zaben 2023 da INEC ta yi abin takaici ne.
"Mun sha mamaki a ranar zabe da muka gano INEC ta yi amfani da hoto mai dishi-dishi don wakiltar tambarin jam'iyyar NNPP. Wani abin ban mamaki shine yadda hoton da aka sanya a kan takardar kada kuri'ar bata dauke da sunan jam'iyyar mu.
"Mafi yawancin magoya bayan mu sun gagara tantance NNPP a takardar zaben. Babban alamar da ke wakiltar jam'iyyar mu shine kwandon kayan marmari. Amma a takardun zaben INEC, ba za a iya gane kwandon ko kayan marmari ba. Wannan ba iya rikitar da magoya bayan mu ya yi ba, ya hana su yancinsu na zabe da gangan."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: A Karshe Shugaban INEC Ya Mayar Da Martani Ga Jam'iyyun Adawa

Alkali ya kara da cewa idan ana domin yin adalci, INEC ta dage tattara sakamakon zabe kuma ta fitar da wani ranar da za a ayi sabon zabe.

Jihohin da Asiwaju Bola Tinubu ya lashe a zaben shugaban kasa na 2023

A bangare guda kun ji cewa hukumar zabe, INEC, ta tabbatar da Asiwaju Bola Tinubu na APC a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.

Hakan na zuwa ne a yayin da wasu jam'iyyun adawa suka nuna rashin amincewarsu da zaben.

INEC ta sanar da hakan ne bayan kamalla tattara sakamakon zabe daga jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164