Zaben 2023: Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Zanga-Zanga
- Gwamnatin Kaduna ta ce dokar haramta zanga-zanga a jihar tana nan daram a cigaba da tattara sakamakon zabe
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya ce duk wanda yayi yunkurin tada hargitsi jami'an tsaro za su dauki matakin da ya dace
- Gwamnatin Kaduna ta kuma yabawa al'ummar jihar kan yadda suka fito zabe cikin tsari da kwanciyar hankali
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce dokar haramta zanga-zanga a jihar tana nan daram yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zabe a jihar, Premium Time ta rahoto.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shi ne ya sanar da haka ranar Lahadi a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aruwan ya ce gwamnatin ta gamsu, matuka, da yadda aka gudanar da zabe lafiya ta kuma yabawa al'ummar jihar bisa yadda suka fito zabe cikin tsari.
''Sobada haka, dole ne mazauna gari, su guji zanga-zanga saboda sakamakon zabe ko ma kowacce irin zanga-zanga don tabbatar da cigaban zaman lafiya. Duk wani abu da zai tayar da hargitsi jami'an tsaro za su dauki matakin da ya dace.
''Ya kamata kowa ya sani sanar da sakamakon zabe alhakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ne.''
Ya kuma bayyana cewa duk wani mutum ko wata kungiya da ke sanar da sakamakon zabe su sani suna kawo barazana ga zaman lafiyar al'umma.
''Duk wani mutum ko kungiya da yake da shakku kan sakamakon zabe su dauki mataki na shari'a kamar yadda dokar zabe ta tanada''.
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Elrufai yana sanya ido akan yanayin tsaro a jihar kan abin da ya shafi zabe tare da hukumomin tsaro a jihar.
2023: Jihohin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar cin zabe
A bangare guda kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta tabbatar da Asiwaju Bola Tinubu na APC a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.
Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Sheikh Bala Lau Ya Gargadi Yan Siyasa Kan Furta Maganganu Da Ka Iya Tada Rikici
Hakan na zuwa ne a yayin da wasu jam'iyyun adawa suka nuna rashin amincewarsu da zaben.
INEC ta sanar da hakan ne bayan kamalla tattara sakamakon zabe daga jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng