Jam’iyyar Labour Ta Lashe Kujerar Majalisa Ta Farko a Zaben 2023 Daga Jihar Abia
- A karon farko, jam'iyyar Labour ta samu nasarar lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta kasa a jihar Abia
- Wannan na zuwa ne a sakamakon zaben da hukumar zabe a jihar ta sanar bayan tattarawa da kirga adadin kuri'un
- Ana ci gaba da tattara sakamakon zabe a Najeriya, jihohi na ci gaba da kawo sakamakon abin da jama'a suka wuni suna kadawa
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Hon, Ginger Onwusibe na jam’iyyar Labour a matsayin zababben dan majalisar wakilai na tarayya a mazabar Isialangwa ta Arewa da Kudu a jihar Abia.
Ginger, wanda tsohon shugaban karamar hukuma ne ya buge dan takarar da gwamna Okizie Ikpeazu ke goyon baya; Farfesa Anthony Agbazuere, rahoton Daily Trust.
Dan takarar na LP ya samu kuri’u 20,411 masu kyau yayin da abokin mahayyarsa a PDP ya samu 13,508.
Ya lallasa dan takarar PDP da ya fi sanuwa
Ginger ya lallasa dan takarar na PDP, Farfesa Agbazuere har a karamar hukumarsa ta Isialangwa ta Kudu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin da ake ciki, mabiya jam’iyyar Labour na ci gaba da murna da farin cikin wannan nasarar da suka samu.
Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Najerya.
An samu tashin hankali a wasu jihohin kasar, inda 'yan daba suka dinga farmaki jama'a masu kada kuri'u ba gaira babu dalili yankuna daban-daban na kasar.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour na ci gaba da samun kuri'u a fannoni daban-daban na Najeriya.
An farmaki ofishin INEC a jihar Kano, kadan ya hada a kone shi
A wani labarin, kunji yadda wasu 'yan daba suka farmaki ofishin zabe na hukumar INEC a karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Wannan lamarin ya zo da tsaiko, inda aka ruwaito cewa, akalla mutum hudu sun mutu yayin da 'yan daban suka kokarin bankawa ofishin wuta da safiyar ranar Lahadi.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi martani, ta kuma bayyana yadda lamarin ya faru, sai dai bata bayyana labarin mutuwar mutum hudu da aka ce sun mutu a farmakin ba.
Asali: Legit.ng