INEC Ta Bude Zauren Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 a Najeriya

INEC Ta Bude Zauren Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 a Najeriya

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta fara karbar sakamakon zaben bana a hukumance a birnin tarayya Abuja
  • Hukumar ta bayyana yadda za ta yi aikin karbar sakamakon zaben ba tare da wata matsala ba
  • A jiya ne aka kada kuri’a a Najeriya, ana jiran sanin wanda zai gaji Buhari a zaben 2023 na bana

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da zauren karbar sakamakon zaben shugaban kasa na Najeriya na 2023 a hukumance.

Wannan batu na fitowa ne daga bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, inda ya bayyana shirin hukumar a bana, BBC ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana cewa, a hukumance za a fara tattara sakamakon zaben daga yankuna daban-daban na Najeriya tare da sanarwa duniya.

INEC ta bude wurin tattara sakamakon zabe
Yadda INEC ta shirya karbar sakamakon zabe | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sakamakon da za a tattara

Kara karanta wannan

Tambuwal Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Karbi Sakamakon Zaben 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, aikin tattarawar zai hada ne daga gundumomi, kananan hukumomi kana za a kai ga matakin jiha-jiha.

Wannan shiri dai na INEC a Abuja za a yi shiri gaba daya, inda aka saba tattara sakamkon zaben shugaban kasa a duk shekarar da aka yi zabe.

Yadda za a tattara sakamakon zaben bana

Farfesa ya ce, duk baturen zaben da ya zo daga jihar da yake wakilta zai karanta sakamakon zaben ne yadda kowa zai ji ta hanyar fadin kuri’u da duk abin da ya faru.

A haka, shugaban yace za a tattara sakamakon zaben kowace jiha, inda daga baya za a kira wakilan jam’iyya su sanya hannun kan sakamakon zaben.

Wannan ne zai ba ‘yan jarida da kuma wakilan jam’iyyun siyasa tabbatar da gaskiya da kuma zaba shaidu kan sakamakon da aka gabatar.

Kara karanta wannan

Assha: EFCC ta kame daraktan kamfen gwamnan PDP na Arewa da kudade a hanyar zuwa zabe

Da yake gargadi, ya ce babu wani wuri da a hukumance da hukumar ke tattara sakamakon zabe face wannan zaure da ya kawo.

An kone akwatunan zabe a wata jiha

A jihar Edo kuwa, an samu tsaiko yayin da wasu ‘yan daba suka kone akwatunan zaben da aka cike da kuri’u a zaben jiya.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wannan lamari ya faru ne bayan da mutanen gari suka gama jefa kuri’a a wata rumfar cikin Benin.

An samu tsaiko da yawa a wasu rumfunan zabe a Najeriya, hakan ya jawo cece-kuce da tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.