EFCC Ta Kama Malamin Jami'ar Najeriya Da Tsabar Kudi N306k A Rumfar Zabe

EFCC Ta Kama Malamin Jami'ar Najeriya Da Tsabar Kudi N306k A Rumfar Zabe

  • Hukumar yaki da rashawa da masu yi wa arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama wani lakara na Jami'ar Saruwan Tarka da ke Benue kan zargin siyan kuri'u
  • An kama Dr Dr Cletus Tyokyya dauke da tsabar makuden naira 306,700 a cikin motarsa ya taho wata rumfar zabe da ba nasa ba
  • Bayan ya shiga hannu, jami'an na EFCC sun nemi ya yi bayanin yadda abin da ya kawo shi rumfar da ba tashi ba da makuden kudi amma ya yi ta kame-kame

Jihar Benue - Hukumar yaki da masu yi wa kasa ta'annati, EFCC, ta ce jami'anta da ke sa ido kan zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya, sun kama wasu da ake zargi da siyan kuri'u a Benue.

Taswirar Jihar Benue
Taswirar Jihar Benue. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Daga sintirin sa ido: 'Yan daba sun yi kaca-kaca da tawagar EFCC a filin zabe a Abuja

EFCC din cikin sanarwa da suka fitar ta ce an kama wani lakcara da ke aiki a Jami'ar Sarwuan Tarka (tsohuwar Jami'ar Noma), a Makurdi, Jihar Benue, dauke da N306,700 a cikin motarsa, Premium Times ta rahoto.

Sanarwar kakakin hukumar Wilson Uwujaren ta fitar a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu ya ce:

"Jami'an hukumar EFCC da ke sa ido kan zaben shugaban kasa da majalisar tarayya sun kama wasu mutane da ake zargin masu siyan kuri'u ne.
"An kama wani Dr Cletus Tyokyya, lakcara a Jami'ar Sarwuan Tarka (tsohuwar Jami'ar Noma), a Makurdi, Jihar Benue, a akwatin zabe na RCM a Daudu, karamar hukumar Guma a jihar dauke da tsabar kudi N306,700 a cikin motarsa."

Ya yi rashin sa'a ne lokacin da ya taho rumafar zabe wacce ba tashi bane kuma ya yi kokarin tserewa bayan ya hango jami'an na EFCC.

Amsar da Dr Tyokyya ya bada

Kara karanta wannan

Assha: EFCC ta kame daraktan kamfen gwamnan PDP na Arewa da kudade a hanyar zuwa zabe

Da aka tambaye shi abin da ya kawo shi rumfar zaben, Dr Tyokyaa ya gaza bada bayani mai gamsarwa, hakan yasa aka kama shi, aka bincika motarsa kuma aka gano kudade daban-daban.

Daga bisani an sake shi bayan ya ba wa hukumar jawabi.

An kama wani mutum dauke da miliyoyin naira na sabbi da tsaffin kudi zai kai wa dan siyasa a Gombe

A wani rahoton hukumar ICPC ta kama wani mutum mai suna Hassan Ahmed da tsabar takardun kudi da suka kai miliyan biyu da ya ce zai kai wa wani dan siyasa ne a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164