Kansila Ta Yi Jarumta Ta Tsere Daga Sansanin Yan Bindiga Da Suka Sace Ta
- Wata kansila ta kubuta daga hannun yan garkuwa bayan shafe kwana hudu a hannun su
- Kansilar da ke wakiltar mazabar Kabwir-Fadar a Filato ta samu kubucewa a hannun masu garkuwar a Jihar Bauchi
- Rundunar yan sandan Jihar ta ce bata da cikakkaiyar masaniya kan lamarin saboda suna kan aikin gudanar da zabe a halin yanzu
Jihar Plateau - Wata kansila a Jihar Filato, Hannatu Bawa, da yan bindiga suka yi garkuwa da ita ta kubuta daga hannun masu garkuwa da ita.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kansilar mai wakiltar mazabar Kabwir-Fadar da ke karamar hukumar Kanke an yi garkuwa da ita ne har gida.
Bayan garkuwa da Bawa, an tafi da ita zuwa makwabciyar Jihar Bauchi inda ta kubuta bayan shafe kusan kwana hudu a hannun su.
Wani mazaunin garin Bauchi ya tabbatar da kubutar kansilar
Wani mazaunin karamar hukumar Kanke, Moses Bap ya tabbatar da kubutar kansilar daga hannun yan garkuwar ga jaridar Punch a Jos ranar Asabar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bap, ya bayyana cewa an kai ta asibiti tana karbar magani a halin yanzu.
Bap ya ce:
''Zan iya tabbatar mu ku kansilar mu ta shaki iskar yanci. Daga abin da naji, ta kubuta daga hannun yan garkuwar a Das da ke Bauchi inda ta dinga gudu cikin daji kafin ta isa cikin garin Boi shima a Jihar Bauchi.
''Daga nan ta kira shugaban karamar hukumar Kanke, Henry Gotip wanda ya tura jami'an yan sanda da sauran jami'an tsaro don ceto ta. Yanzu haka tana asibiti tana karbar magani saboda wahalar da ta sha a hannun yan garkuwar.''
Martanin yan sandan jihar Filato
Mai magana da yawun yan sandan Jihar Filato, Alabo Alfred ya ce basu samu masaniya akan yadda kansilar ta kubuta ba
A cewar mai magana da yawun yan sandan:
''Zan ji bayani idan na karbi rahoton yadda aka ceto ta. A yadda labarin ke da muhimmanci, yanzu muna kan gudanar da aikin zabe dan tabbatar da ba a samu matsalar tsaro a jihar ba."
An kama wani mutum dauke da miliyoyin naira na sabbi da tsaffin kudi zai kai wa dan siyasa a Gombe
A wani rahoton kun ji cewa hukumar yaki da rashawa na ICPC ta kama wani Hassan Ahmed da makuden takardun naira da suka hada da sabbi da tsaffi a yayin da al'umma ke fama da karancin kudi.
Sojoji na 33 Artillery Brigade da ke aikin sintiri a Alkaleri Bauchi ne suka damke mutumin da kudaden cikin jaka ta 'Ghana must go' sannan suka kai shi wurin ICPC.
Asali: Legit.ng