El-Rufai Ya Yiwa Tinubu Addu’ar Allah Ya Bashi Nasara a Zaben Bana
- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa, yana rokon Allah ya ba Tinubu nasara a zaben bana da aka yi
- Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kada kuri’arsa a jihar Kaduna bayan bin dogon layi kamar yadda kowa ya yi
- Ya kuma bayyana kadan daga kalubalen da aka samu na tsaiko a zaben, amma ya yabawa INEC bisa jajircewa da tsara komai cikin sauki
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi addu’ar Allah ya ba dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu nasara a zaben bana, The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bi dogon layi na tsawon awa guda kana ya kada kuri’arsa a rumfar da yake zabe.
Ya kuma bayyana damuwarsa ga karancin masu kada kuri’a a zagayen jihar Kaduna da kuma masu sace na’urar BVAS a yankuna daban-daban na kasar.
A fito a yi zabe, El-Rufai ga jama’ar jiharsa
Ya yi kira ga mazauna jihar Kaduna da su fito su kada kuri’a kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya basu, Channels Tv ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A jawabansa, cewa ya yi:
“Mun godewa Allah da ya nuna mana wannan rana da dukkan ‘yan Najeriya za su zabi wanda mulke su na tsawon shekaru hudu.
“A jihar Kaduna ya zuwa yanzu, ya zuwa lokacin da na zo nan, komai na tafiya daidai.
“Sa safen nan, mun samu rahoton wani lamari a Kudancin Kaduna inda aka sace na’urar BVAS da akwatin zabe da kuma a Soba inda aka sace akwatunan zabe guda biyu.”
Duk da faruwar wasu abubuwa marasa dadi a jihar, gwamnan ya kuma yabawa hukumar zabe ta INEC bisa jajircewa da tsayawa tsayin daka ga faruwar zaben bana
Rahotanni sun nuna yadda ‘yan siyasa da dama suka kada kuri’unsu cikin tsanaki a bagarori daban-daban na Najeriya.
Tinubu Ya Yi Nasara a Rumfar da Ya Kada Kuri’a a Jihar Legas, Atiku Ya Samu Kuri’a 1
A wani labarin, kun ji yadda Tinubu ya samu nasara a rumfar da ya kada kuri’arsa da sanyin safiyar yau Asabar 25 ga watan Faburairu.
An bayyana cewa, ya samu kuri’u 33 yayin da Atiku kuma ya samu 1, Peter Obi ya samu kuri’u 8.
Ana ci gaba da samun rahotanni kan sakamakon zaben 2023 da aka yi a yau Asabar.
Asali: Legit.ng