Yan Ta'adda Sun Kai Hari Rumfar Zabe, Sun Banka Wa Akwatin Zabe Wuta
- Wasu yan daban siyasa dauke da bindigu da muggan makamai sun kai wasu wasu rumfunan zabe a Jihar Legas
- Rahotanni sun nuna cewa wuraren da abin ya shafa sun hada da unguwar Oshodi da Otire, inda maharan suka fatattaki jama'a kafin suka kona akwatin zabe
- Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun kai hare-haren ne yan mintuna bayan da jami'an tsaro masu aikin zabe suka bar rumfunan zaben
Jihar Legas - Wasu yan daba dauke da bindigu sun kai hari rumfunan zabe a Oshodi da Itire a Legas, inda suka kona akwatunan zabe.
Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun taho ne sanya da bakaken tufafi da face mask misalin karfe 11.30 na safiyar ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu masu zabe da ba su iya tserewa ba a lokacin da yan daban suka iso sun jikkata.
Wasu majiyoyi sun ce yan ta'addan sun kai farkamin ne yan mintuna bayan jami'an tsaro da ke aikin zabe sun bar wuraren.
A cewar wani Tajudeen Haruna, bayan yan mintuna, yan daban sun bude wuta don tsorata masu zabe.
Ya cigaba da cewa:
"Daga baya ne yan ta'addan suka cinna wa akwatin zaben da sauran kayan zabe wuta."
Hakazalika, wasu yan ta'adda sun kai hari a unguwar Itire, misalin karfe 12 na rana, suka tsorata mutane da masu zabe a yankin.
James Nwoke, ya yi ikirarin cewa an yi hakan da gangan ne don haka wasu mutane zabe.
Amma, akwai yan sanda da dama da sojoji a birnin Legas a ranar Asabar don kiyayye rushewar doka da oda.
A bangare guda, wasu matasa sun mayar da hanyar Agege da Apapa-Oshodi da wasu yankunan Ago palace zuwa filin kwallo.
Ana zullumi a mafi yankuna da ke Ago, Isolo da Ire-Akri bayan wasu sun gaza gana akwatunan zaben su.
An kama wani mutum dauke da miliyoyin naira na sabbi da tsaffin kudi zai kai wa dan siyasa a Gombe
A wani rahoton kun ji cewa hukumar yaki da rashawa na ICPC ta kama wani Hassan Ahmed da makuden takardun naira da suka hada da sabbi da tsaffi a yayin da al'umma ke fama da karancin kudi.
Sojoji na 33 Artillery Brigade da ke aikin sintiri a Alkaleri Bauchi ne suka damke mutumin da kudaden cikin jaka ta 'Ghana must go' sannan suka kai shi wurin ICPC.
Asali: Legit.ng