Yanzu nan: Abba Kyari Ya San Matsayarsa a Kotu, Alkali Ya ce Zai Yi Zabe a Kurkuku
- Lauyoyin Abba Kyari ba su yi nasara wajen nema masa beli a babban kotun daukaka kara ba
- Alkalan babban Kotun sun zartar da hukunci cewa za a cigaba da tsare babban jami’in ‘dan sandan
- DCP Kyari ya shiga hannu ne a kan zargin mu’amala da miyagun kwayoyi tun a shekarar 2022
Abuja - Kokarin neman belin da Abba Kyari yake yi bai yi nasara ba, domin a ranar Juma’ar nan kotun daukaka kara tayi watsi da wannan roko.
A yau Punch ta rahoto cewa DCP Abba Kyari bai yi nasara a karar da ya shigar a gaban babban kotun daukaka kara da ke zama a garin Abuja.
Jami’in ‘dan sandan da aka dakatar daga bakin aiki ya nemi Alkali ya ruguza shari’ar babban kotun tarayya da ke zama a Abuja da ta hana shi beli.
Da ya saurari karar dazu, Mai shari’a Stephen Adah ya zartar da hukunci cewa ba za a iya ba ‘dan sandan beli ba ganin irin zargin da ke wuyansa.
Stephen Adah ya amince da hukuncin Emeka Nwite
A madadin sauran Alkalai uku da suka yi shari’ar, Alkali Adah ya ba Emeka Nwite na otun tarayya gaskiya, ya ce ka da a saki jami’in ‘dan sandan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta tabbatar da cewa dole ayi hattara a wajen sakin tsohon shugaban dakarun IRT daga gidan kaso, hakan yana nufin za a cigaba da tsare shi.
Sauran da ake tuhuma da laifin harkar kwayoyi sun hada da ACP Sunday J. Ubua, ASP Bawa James, Sufeta Simon Agirgba da Sufeta John Nuhu.
Vanguard ta ce kotun daukaka kara tayi fatali da bukatar Lauyoyin Kyari, ta jadadda hukuncin karamar kotun da ta saurari wannan shari’a a baya.
Kyari wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne ya shiga hannun NDLEA da zargin ya taba wasu kilogram 21.35 na hodar iblis da aka karbe.
Tun farko da ‘dan sandan ya nemi kotu ta bada belinsa, Alkali Emeka Nwite bai amince ba. Ganin bai yadda da shari’ar ba, sai ya daukaka kara.
Kyari ya na kalubalantar NDLEA
Da kotu ta zauna a watan Junairu, an ji labari DCP Kyari ya yi da’awar NDLEA ba ta da hurumin yin shari’a da shi, domin 'yan sanda na bincikensa.
Amma NDLEA tayi raddi, ta ce binciken ‘yan sanda ba zai hana ayi shari’a da su Kyari a kotu ba. Nureni Jimoh SAN shi ne Lauyan Hukumar a gaban kotu.
Asali: Legit.ng