Mutane 15 Sun Mutu, 7 Sun Jikkata A Wani Hatsarin Mota Da Ya Faru A Bauchi
- Wani mummunan hadarin mota ya ci rayukan mutum 15 tare da raunata mutum 7
- Hadarin wanda arangama ce tsakanin karamar motar haya da kuma tirelar Dangote ya faru da yammacin Alhamis a garin Nabardo
- Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta ce hadarin ya faru sakamakon gudun wuce sa'a da kuma tukin ganganci wanda ya janyo direban ya kasa sarrafa motar
Jihar Bauchi - Wani mummunan hadarin da ya auku a ranar Alhamis a garin Nabardo da ke titin Bauchi-Jos a karamar hukumar Toro da ke Jihar Bauchi ya yi sanadin rasuwar mutane 15, Leadership ta rahoto.
Karin wasu mutum bakwai sun ji rauni iri daban daban a hadarin da ya auku sanadiyar gudun wuce sa'a da kuma tukin ganganci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hadarin da ya hada da motocin haya guda biyu, mota kirar Toyota Hiace mai lambar mota: YLA 984XA mallakin Adamawa Sunshine da kuma babbar tirela mai lamba: DKD 33XB mallakar kamfanin Dangote.
Kwamandan FRSC na Jihar Bauchi ya magantu kan hadarin
Babban kwamanda, hukumar kiyaye hadura ta kasa, reshen Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi ya tabbatarwa majiyarmu faruwar lamarin da daren Alhamis, The Punch ta rahoto.
Ya ce:
''Eh, an samu hadari yau, Alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023. Lamarin ya faru a garin Nabardo da ke karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi.
''Ya hada da motoci biyu mallakar kamfanin Adamawa Sunshine da kuma tirelar Dangote. Hadarin ya faru da misalin 3.45 na yamma kuma jami'an mu sun isa wajen cikin mintuna takwas don aikin ceto.
''Jimullar mutum 22, mata biyu manyan, maza manya 18, da kananan yara mace da namiji, su ne wanda hadarin ya rutsa da su sanadiyar gudun wuce sa'a da kuma tukin ganganci wanda ya janyo direban ya kasa sarrafa motar."
Ya cigaba da cewa:
''Jami'an sun kwashe wanda abin ya shafa zuwa Asibitin koyarwa na jami'ar Tafawa Balewa, Bauchi don basu taimakon gaggawa da kuma tabbatar da wanda suka mutu.
''A nan ne likita ya tabbatar da mutuwar mutum 15, maza 12, mace daya, kananan yara mace da namiji. Maza shida da mace daya sun ji rauni iri daban daban.''
Shugaban FRSC ya bayyana cewa an adana gawarwakin a dakin adana gawa na Asibitin koyarwar kafin a baiwa iyalan su don binne mamatan.
Ya yi bayanin cewa sun gudunar da aikin agajin da hadin gwiwar jami'an hukumar yan sandan Najeriya.
A wani rahoton kun ji cewa Mrs Dorcas Afeniforo, kwamishinan ma'aikatan kula da ma'aikatan jihar Kwara ta rasu a hadarin mota.
Tsohuwar kwamishinan na harkokin mata kuma cikin na kusa da gwamnan Kwaran ta rasu ne a ranar Asabar yayin dawowa daga Legas.
Asali: Legit.ng