Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Kwamishinan Jihar Kwara Ta Rasu A Hadarin Mota

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Kwamishinan Jihar Kwara Ta Rasu A Hadarin Mota

  • Gwamnati da al'ummar jihar Kwara sun shiga zaman makoki sakamakon mutuwar Mrs Dorcas Afeniforo, kwamishina mai kula da ma'aikatan gwamnatin jiha
  • Rafiu Adekoye, Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Kwara ya tabbatar Mrs Afeniforo ta rasu a hadarin mota
  • Tsohuwar kwamishinan kula da harkokin matan ta rasu ne a ranar Asabar a hanyarta na dawowa daga jihar Legas

Jihar Kwara - Kwamishina a ma’aikatan kula da ma’aikatan gwamnatin jihar Kwara, Mrs Dorcas Afeniforo ta riga mu gidan gaskiya, rahoton jaridar Punch.

Mrs Afeniforo, tsohuwar kwamishinan harkokin mata kuma daya cikin masu yi wa gwamna biyayya, ta rasu ne a hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawo wa daga tafiya a jihar Legas.

Jihar Kwara
Allah Ya Yi Wa Kwamishinan Jihar Kwara Rasuwa A Hadarin Mota. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Sauya Kudi: Da Gaske Gwamnan CBN Na Son Haddasa Rudani a Zaben 2023? Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu

Gwamnan Jihar Kwara, Mallam Abdulrahman AbdulRazaq cikin wata sanarwa da babban sakataren watsa labaransa, Mr Rafiu Ajakaye, ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana mutuwar marigayiyar mai rajin kawo cigaban matan a matsayin abu mai ciwo da ban girgizawa.

Gwamnan cikin sanarwar ya ce:

“Abin da ya faru yana da ciwo da girgizaya wa. Babban rashi ne ga jam’iyyar masu son kawo cigaba a jihar.
Za a cigaba da tunawa da Mrs Afeniforo saboda ayyukan ta na alheri a matsayin jigo na kawo cigaba a harkokin mata a jihar.
“Muna mika ta’aziyya ga iyalan Mrs Afeniforo da mutanen kirki na Baruten da Kwara north wadanda ta wakilta a CSC zuwa rasuwarta.
"Muna addu’a Allah ya gafarta mata ya ba wa iyalanta hakurin jure rashinta”.

Hadarin Mota Ya Yi Sanadin Rasuwar Mutane 15 A Jihar Kogi, Wasu Mutane 5 Sun Samu Munanan Rauni

A wani rahoton, hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, ta tabbatar da cewa kimanin mutane 15 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota da ya faru a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hadarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar J-5 da babban tankan dakon man fetur da Koton-karfe da ke babban hanyar Lokoja-Abuja.

Mr Stephen Dawulung, babban kwamandan hukumar FRSC na jihar Kogi, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an garzaya da mutane biyar din da suka jikkata zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel