Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’
- Ministan shari’a ya bayyana kokarin tsabtace zaben Najeriya a matsayin makasudin canza kudi
- Abubakar Malami SAN ya ce Muhammadu Buhari yana burin hana amfani da kudi wajen yin magudi
- Babban lauyan gwamnatin kasar ya nuna akwai yiwuwar a binciki Gwamnonin da suke rigima tsarin
Abuja - Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami ya yi maganar wadanda suka rika sakin baki a kan canjin kudi.
A dalilin tsarin canza takardun Naira da aka yi, wasu mutane har da Gwamnoni sun yi ta maganganu, Daily Trust ta rahoto cewa ana shirin bincike.
Abubakar Malami SAN ya shaida cewa jami’an tsaro za su dauki mataki bayan sun kammala binciken wadannan mutane da zargin cin amanar kasa.
Ministan shari’a na kasa ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyi daga wajen ‘yan jarida a fadar shugaban kasa na Aso Villa a ranar Alhamis.
Gwamnoni sun ja daga da gwamnati
Rahoton ya ce a cikin Gwamnonin jihohi, Mai Girma Nasir El-Rufai da Abdullahi Umar Ganduje sun fi kowa sukar tsarin nan da bankin CBN ya fito da shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abin ya kai sai da wasu Gwamnoni suka shigar da karar gwamnatin tarayya a kotun koli.
AGF: 'Akwai zargin cin amanar kasa'
Da ake zantawa da shi, Malami SAN bai ambaci sunan kowane Gwamna ba, amma ya ce kalamansu za su iya zama cin amanar kasa, kuma za a bincike su.
Mai girma Ministan yake cewa jami’an tsaro za su yi wannan bincike, sannan a yanke hukunci idan har akwai wani mataki na gaba da ya dace a dauka.
A jawabinsa, Ministan ya sake jaddada matsayar gwamnati na cewa wasu daidaikun mutane ne suka saci kudi, ana kokarin amfani da shi wajen murde zabe.
A matsayinsa na AGF, Malami ya ce canza kudin zai ba al’umma damar ganin wanda suke kauna ya lashe zabe, a maimakon attajirai suyi amfani da dukiya.
Ministan ya ce makasudin tsarin shi ne a tsabtace zabe domin gwamnati ta na kokarin kawo gyara. Jaridar nan ta This Day ta fitar da wannan labari.
Akwai yiwuwar binciken masu sakin kalamai, Ministan kasar ya ce wannan aikin jami’an tsaro ne, daga nan sai a dauki matakin laifin da ya kira bore.
'Ina shan wahala' - Orji Uzor Kalu
Duk da yana Sanata a Majalisar dattawa, an samu labari kwanakin baya Orji Uzor Kalu ya ce sun gagara dafa abinci a gidansa dalilin rashin kudi.
Sanata Kalu ya ce tsarin canza kudin daidai ne, amma yana shan wahala saboda bai ajiye kudi a gidansa, ya ce ko maroka sun zo, bai iya ba su komai.
Asali: Legit.ng