'Yan Bindiga Sun Sace Matar Basarake a Jihar Imo, Sun Kone Gidajen Shugabannin APC da LP
- Yayin da zabe ya karato, ana ci gaba da samun ayyukan ta’addanci a yankuna daban-daban na kasar nan
- An sace wata matar basarake a jihar Imo a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai mummunan farmaki kan mazauna
- An kone gidan shugaban jam’iyyar Labour da APC, majiya ta bayyana dalla-dalla yadda lamarin ya faru
Okigwe, jihar Imo - Wasu tsagerun ‘yan bindiga a ranar Laraba sun sace matar basaraken Amuro na karamar hukumar Okigwe a jihar Imo, Uzoeze Umugborogu.
Bayan sace matar basaraken, tsagerun ‘yan bindigan sun kuma kone gidajen shugabannin jam’iyyun APC da LP na gundumar Amuro.
Wannan lamari dai ya haifar da rikici da tashin hankali a yankin, inda mazauna suka dinga fita daga gidajensu suna tserewa.
Yadda lamarin ya faru daga bakin wani ganau
Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, ‘yan bindigan sun kone gidajen ne a daidai lokacin da suka isa yankin, rahoton Punch.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar majiyar:
“An sace matar marigayi sarkin Amuro mai karfin iko, Ugoeze Umugborogu
“Bayan sace matar, sun zarce gidan shugaban jam’iyyar Labour na gundumar Amuro, Ifediora Umugborogu suka kone shi. Mutumin da ahalinsa ba sa nan lokacin da aka kai farmakin.
“Haka kuma sun kone gidan shugaban jam’iyyar APC na gundumar. Wannan abin ya fara wuce gona da iri. Ya kamata gwamnati ta kawo mana dauki.”
Ana ta’addanci a Okigwe
Karamar hukumar Okigwe na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kwanakin nan.
A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kone gidajen jama’a a gundumar Amagu Ihube na karamar hukumar, ciki har da gidan kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Emeka Okoronkwo, Daily Report ta tattaro.
Hakazalika, sun kone gidajen tsohon shugaban tsangayar ilimin shari’a na jami’ar jihar Imo, Nnamdi Obiaraeri da kuma tsohon daraktan hukumar DSS, Nnaemeka Ngwu.
An kone gidan rediyo da TV a jihar Ribas
A wani labarin kuma, wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan wani gidan talabijin da rediyo a wani yankin jihar Ribas.
Wannan lamarin da ya zo a ranar Talata ya tada hankalin jama’a da ma’aikatan gidan talabijin din.
Mai gidan yada labaran ya shaida cewa, ba a samu wani wanda ya ji rauni ba ko kuma asarar rai.
Asali: Legit.ng