Ganin an Canza Nairori, ‘Yan Siyasa Sun Fito da Sabon Dabarar Yin Magudi Inji EFCC

Ganin an Canza Nairori, ‘Yan Siyasa Sun Fito da Sabon Dabarar Yin Magudi Inji EFCC

  • Shugaban Hukumar EFCC ya ce saboda an canza kudi, ‘yan siyasa sun koma sayen kayan rabawa
  • Abdulrasheed Bawa ya shaidawa Duniya cewa za su yaki sayen kuri’u da ‘yan siyasa za suyi a zabe
  • Hukumar tana neman hadin-kan mutane domin maganin masu amfani da kudi wajen samun kuri’a

Abuja - Abdulrasheed Bawa wanda yake rike da shugabancin hukumar EFCC, ya ce ‘yan siyasa sun yi niyyar sayen kuri’un talakawa a zabe mai zuwa.

Da aka zanta da shi a tashar talabijin na Channels a ranar Laraba, Abdulrasheed Bawa ya zargi mutane da boye kudi saboda ayi magudi a zaben bana.

Shugaban na EFCC yake cewa ba zai so ya kebe ‘yan siyasa kurum da zargin ba, domin akwai sauran mutane da suke boye makudan kudi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Amurka Ya Aikowa 'Yan Najeriya da Sako Za a Shiga Filin Zabe

Masu ruwa da tsaki sun koka cewa idan aka yi amfani da kudi, ba za ayi zaben adalci da gaskiya ba. Rahoton nan ya fito a jaridar The Cable a ranar Laraba.

"Za a rabawa masu zabe kaya" - EFCC

Bawa ya nuna cewa yanzu ‘yan siyasa su na so su fanshi kuri’un jama’a ne ta hanyar raba masu kaya a maimakon kudi tun da ba a samun takardun sababbin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A tattaunawar da aka yi da shi, Business Day ta rahoto cewa Abdulrasheed Bawa ya yi kira ga al’umma su ba su hadin-kai wajen yaki da sayen kuri’un zabe.

EFCC.
Hedikwatar EFCC Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Mista Bawa ya ce bayanai sun zo masu cewa karancin kudi ya jawo masu neman mulki sun tanadi kayan da suke so su rabawa wadanda ke kada kuri’a.

“Kwarai, mun samu bayanan sirri cewa mutane da-dama sun sayo wasu kayayyaki da suke so su rabawa mutane a maimakon kudi.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Sarki Sanusi ya tona asirin abin da aka kitsa wajen sauya fasalin Naira

Wadannan duk su na faruwa a yanzu. Za mu sa masu ido domin mu gani. ‘Yan siyasa su ma ‘Yan Najeriya wanda suka kware a aikinsu.
Mu ma hukumar EFCC mu na da hanyar da mu ke bi wajen yin irin ayyukanmu."

- Abdulrasheed Bawa

Punch ta rahoto babban jami’in yana cewa sun san halin da jama’a suka shiga, amma ya ce tsarin da aka dauko zai yi sanadiyyar tsabtace harkar zabe a kasar.

Okezie Ikpeazu ya karyata Orji Kalu

Ku na da labari Gwamnan jihar Abia, Dr. Okezie Ikpeazu ya karyata jita-jitar marawa APC baya a zaben 2023 yayin da yake cikakken ‘dan jam’iyyar hamayya.

Sanannen lamari ne Gwamnonin jihohin Ribas, Abia, Enugu, Oyo da Benuwai ba su tare da jam’iyyarsu, ba za su goyi bayan Atiku Abubakar a zaben bana ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng