IGP Usman Baba Ya Bada Umurnin Takaita Zirga-Zirga A Ranar Zabe

IGP Usman Baba Ya Bada Umurnin Takaita Zirga-Zirga A Ranar Zabe

  • Shugaban yan sandan Najeriya, Usman Baba ya bada sabon umurni, ana kwana uku zaben shugaban kasa na 2023
  • IGP Baba ya bada umurnin takaita dukkan zirga-zirgan ababen hawa a tituna, ruwa da sauran nau'ikan zirga-zirga
  • An bada umurnin ne domin tabbatar da tsaro da samar da yanayi mai kyau don gudanar da zaben 2023, ta tabbatar da bin doka da oda da tsaron masu zabe da taimakawa jami'an tsaro

A ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya bada umurnin takaita zirga-zirgan ababen hawa a kan tituwa, ruwa da sauran nau'ikan zirga-zirga daga 12.00 na dare zuwa 6 na yammacin ranar zabe.

Wannan umurnin bai shafi masu muhimman aiki ba irin su hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, masu sa ido kan zabe, motoccin asibiti, masu kashe gobarar da sauransu.

Kara karanta wannan

Majalisar Tsaro Ta Kasa Ta Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Ta Bayyana Matsayinta Na Karshe

IGP Usman
IGP Usman Baba Ya Bada Umurnin Takaita Zirga-Zirga A Ranar Zabe. Hoto: Rundunar Yan Sandan Najeriya
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun rundunar yan sandan, Muyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a daren ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu, rahoton da The Punch ta tabbatar.

An shirya yin zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya ne a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Zaben shugaban kasa na 2023: NLC ta dauki mataki na karshe, ta bayyana wanda ma'aikatan Najeriya za su zaba

Gabanin babban zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu na shugaban kasa, kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta ayyana goyon bayan ta ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP.

Kungiyar kwadagon ta ayyana goyon bayan ta ga Obi ne bayan taron da kwamitin shugabanninta na kasa suka yi a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta tattaro cewa goyon bayan da NLC ta yi wa dan takarar shugaban kasar na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakatarenta na kasa, Chris Uyot ya fitar.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Shirin Zabe Na Ta Kankama, Hukumar Zabe Ta INEC Ta Fara Rarraba Muhimman Kayan Aikin Zabe

Tinubu, Atiku da sauran yan takarar shugaban kasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

A wani rahoton, kun ji cewa yan takarar shugaban kasa na jam'iyyu daban-daban a zaben 2023 sun halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da takwararsa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164